Abu bakwai da ya kamata ku yi don tafiya sallar Idi
Sallar Idin ƙaramar salla Ibada ce da Allah Ya shar'anta a matsayin kammala Ibada ta azumin watan Ramadan.
Sallar Idi na ɗaya daga cikin sunnoni masu ƙarfi a addinin musulunci wadda ake yi sau biyu a shekara wato, ƙaramar salla da babbar salla.
Don haka ne ma sallar idin ke buƙatar wasu abubuwa domin yin guzuri a tafiya zuwa masallacin idin.
Dakta Muhammad Nazifi Inuwa wani malamin addini ne a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya bayyana jerin abubuwan da ya kamata mutum ya yi kafin tafiya sallar idi.
Wankan Idi
Wankan Idi ɗaya ne daga cikin wanka na sunnah a addinin musulunci wanda ake yi sau biyu a shekara.
Dakta Muhammad Nazifi Inuwa ya ce an so duk mai tafiya masallacin idi ya gabatar da wankan Idi, domin dacewe da sunnah.
Dangane da wankan, dakta Nazifi ya ce mutum zai iya yin wanka na soso da sabulu domin tsaftace jikinsa, sannan daga baya kuma sai ya yi wankan idin, domin dacewa da ladan sunnar wankan.
Haka kuma malamin ya ce sigar wankan iri ɗaya ne da na sauran wankan addinin muslunci, kamar na janaba, da na ɗaukewar jinin al'ada ko na biƙi, sai dai kawai niyya ce ta bambanta.
Tsaftace jiki
Malamin ya ce tsafta na daga cikin ladubban addinin musulunci, don haka kasancewar ranar Idi rana ce ta musamman, yana da kyau mutum ya ƙara tsaftace jikinsa.
''Wannan ko ya haɗar da aske gashin hammata da na gaba, da aske ƙumba ko farce'', in ji Dakta Muhammad Nazifi.
Malamin addinin ya ci gaba da cewa ''an so mutum ya tsaftace jikinsa ta yadda zai je masallaci ba tare da ya cutar da masallata, da warin jikinsa ba''.
Cin abinci'
A na taruwa a ci abinci tare da 'yan uwa ranar salla
'Ya kamata a samu wani abu a ci kafin tafiya masallacin idi'
Dakta Muhammadu Nazifi ya ce idin ƙaramar salla da babbar salla ya bambanta ta fuskar cin abinci.
''A idin ƙaramar salla ba a so mutum ya tafi masallaci ba tare da ya ci wani abinci ba, domin kada ya je Idi kamar yana azumi'', in ji Malamin.
Dakta Ibrahim Abdullahi ya ce ''ya kamata a samu wani abu a ci kafin tafiya masallacin idi ko da kuwa dabino ne, ko wani abu ko ruwa''.
''Amma a Idin babbar sallar musamman idan mutum zai yi layya to an so ya jinkirta cin abinci har sai ya dawo daga masallacin Idi, ya yanka dabbar layyarsa a gasa masa wani ɓangare na naman dabbar ya fara da shi'', in ji Dakta Muhammadu Nazifi
Yawaita kabarbari
Dakta Nazifi ya ce ana so mai tafiya masallaci ya ci gaba da kabarbari. Dakta Nazifi ya ce ya zo a cikin ruwayoyi masu yawa na irin kabarbarin da za a riƙa yi.
''Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha illallah Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamdu'', Malamin ya ce haka mutum zai riƙa fada, kuma da sauti mai ƙarfi ta yadda zai jiyar da na kusa da shi.
Malamin ya ce hikimar yin kabarbarin cikin sauti mai ƙarfi shi ne don tunatar da waɗanda suka manta da yin kabarbarin.
Dakta Nazifi ya kuma koka kan abin da ya ce wasu matasa ke yi a lokacin tafiya masallacin idin, inda ya ce sai ka ga wasu matasan sun shagalta da hirarrakin duniya a kan hanyarsu ta tafiya masallacin idin.
'Ba a yin sallar nafila gabanin sallar Idi'
Dakta Nazifi ya ce idan mutum ya isa masallacin Idi, abin da ake son ya yi shi ne ya zauna jiran ƙarasowar liman, tare da ci gaba da kabarbari.
''Ba a yin sallar nafila gabanin sallar Idi don haka abin da ake son mutum ya yi shi ne ya zauna jiran isowar liman, ya kuma ci gaba da kabarbari'', in ji malamin.
Ya ƙara da cewa ''da zarar liman ya iso masallaci babu abin da zai yi kawai sai tayar da sallah ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka kuma ana so a zauna a saurari hudubar liman, bayan kammala sallar, ba a son daga sallame sallah a fice daga masallaci don tafiya gida.
Duk da cewa ba wajibi ba ne, amma malamai na cewa yana daga cikin alherin da Annabi SAW ya yi nuni da shi domin samun albarkar addu'ar musulmi da ake yi a cikin huɗubar.
Sauya hanyar komawa gida
Haka kuma an so mutum idan zai koma gida daga masallacin idi, to inda hali ya sauya hanya, kada ya bi ta hanyar da ya bi wajen zuwa masallacin, a lokacin da ya tashi komawa gida.
Dakta Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo ya ce ''an karbo hadisi daga Jabir ɗan Abdullahi, yana cewa Manzon Allah SAW yana saɓa hanyar zuwa da ta dawowa daga sallar idi''.
Dakta Muhammad Nazifi Inuwa ya shawarci waɗanda gidajensu ke kusa da masallatan Idin da su tafi a ƙafa matuƙar yin hakan ba zai cutar da su ba.
Domin kuwa hakan ma bai fi tsinka jini ba, sannan kuma hakan zai rage cunkoson ababen hawa tare da sauƙaƙa wa jama'a, kamar yadda malamin ya ce.
BBC