PDP Ta Bukaci Sanyawa Buhari Takunkumi

Babbar jam’iyyar adawar Najeriya ta PDP ta bukaci kasashen duniya da su hana shugaban kasa Muhammadu Buhari bizar tafiye tafiye da zaran ya mika mulki ranar 29 ga watan gobe, saboda abinda ta kira kalamansa dangane da zaben shugaban kasar da akayi ranar 25 ga watan Fabarairu. 


Yayin tsokaci akan zaben, Buhari ya bayyana ‘yan adawar Najeriya a matsayin wadanda suka shantake akan cewar zasu samu nasara ba tare da neman goyan bayan jama’a kamar yadda jam’iyarsa ta APC tayi ba. 

Sakataren hulda da jama’a na jam’iyyar Debo Ologunagba yace kalaman shugaban na iya tinzira jama’a da kuma haifar da illa ga zaman lafiyar kasar. 

Ologunagba ya kuma ce kalaman na iya karfafawa alkalai gwuiwa wajen yanke hukunci akan karar da suka shigar a gaban kotu domin kalubalantar sakamakon zaben wanda yace tuni wasu a ciki da wajen kasar ke bayyana shi a matsayin mafi muni a tarihin Najeriya. 

Jam’iyyar PDP tace zaben da akayi bana ya gamu da matsalolin da suka sabawa kundin tsarin mulkin kasa da kuma dokar zabe ta shekarar 1999 da kuma 2022 musamman abinda ya shafi wallafa sakamako daga tashoshin zabe da kuma aikewa da su kai tsaye zuwa cibiyar hukumar ta kasa. 

Kakakin jam’iyyar ya jaddada cewar suna da yakinin cewar basu fadi zabe ba, kamar yadda shugaba Buhari ke fadi, kuma ba zasu bada kai bori ya hau ba duk da barazanar da gwamnatin APC ke musu. 

Jam’iyyar tace ganin yadda Buhari ya yiwa dimokiradiya illa a Najeriya, suna bukatar kasashen duniya da su kakaba masa takunkumi da kuma hana shi da iyalansa tafiye tafiye da zaran ya mika mulki ranar 29 ga wata. 

Ologunagba yace wannan bukatar tasu tayi dai dai da bukatar da shugaba Buhari ya gabatarwa kungiyar kasashen Turai a ranar 17 ga watan Fabarairun shekarar 2022 lokacin da ya ziyarci kungiyar EU a Brussels. 

RFI

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki