Kwamitin Karbar Mulki Na NNPP Na Kano Ya Zargi Gwamna Ganduje da gurgunta Tsarin Karbar mulki

Kwamitin Karbar Mulki na jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, ya zargi gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje mai barin gado da yin zagon kasa ga tsarin mika mulki ga gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf mai jiran gado.


A cewar shugaban kwamitin mika mulki na jam’iyyar NNPP, Farfesa Abdullahi Baffa Bichi, gwamnatin Ganduje ta nuna turjiya da rashin hadin kai tun bayan kafa kwamitin mika mulki na NNPP da zababben gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

Jaridar Nigerian Tracker ta rawaito Bichi yana bayyana cewa kwamitin mika mulki na NNPP ya kafa kananan kwamitoci 33, amma babu daya daga cikin kwamitocin da ya samu hadin kai daga gwamnatin Ganduje. Duk da yunkurin kwamitin mika mulki na jam’iyyar NNPP na shirya taron hadin gwiwa da kwamitin mika mulki na gwamnati mai barin gado, gwamnatin Ganduje ta bukaci su zabi mutane uku ne kawai a taron wanda jam’iyyar NNPP ba ta amince da shi ba.

Bichi ya zargi Gwamna Ganduje da mayar da dukkan sakatarorin dindindin na jihar a wani bangare na kokarinsa na kawo cikas ga tsarin mika mulki a Kano.

Kwamitin rikon kwarya na NNPP ya yi kira ga dukkanin hukumomin  da su ba kwamitin mika mulki tare da mutunta zabin mutanen Kano da suka zabi Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Kwamitin Karbar mulkin na NNPP zai gudanar da taron hadin gwiwa tare da dukkanin sakatarorin dindindin, shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnati, da daraktocin gudanarwa na dukkanin kananan hukumomi 44 daga ranar Talata 2 ga watan Mayu, domin tabbatar da samun saukin aikin. 

"Muna kira ga Gwamna Ganduje da ya mutunta zabin mutanen Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya ba da mulki ga wanda Ya so"

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki