Buhari Zai Bar Najeriya Fiye Da Yadda Ya Same Ta – Fadar Shugaban Kasa
Fadar Shugaban Kasa ta ce a fannin tsaro da habaka tattalin arziki, Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015.
Kakakin Shugaban, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels ranar Talata.
Ya kuma ce karyata batun cewa a tsawon mulkin Buhari na shekara takwas, ya nuna kabilanci wajen nafin wadanda za su shugabanci hukumomin tsaron kasar nan.
A cewarsa, nadin nasu ba shi da wata alaka da addinin, yanki ko kabilar da mutum ya fito wajen nadinsu, an fi la’akari da cancanta tun da dai doka ta ba Shugaban ikon nada duk wanda ya ga dama.
Ya ce, “Ka san cewa akwai wani rahoto da ya ce an fi samun karancin mutanen da aka kashe a 2022 a cikin shekara 12 da suka gabata a sakamakon ayyukan ta’addanci? Mun fa sani a Najeriya cewa alkaluman sun ci gaba da sauka a tsawon shekaru.
“Babu wanda ke son a sami asarar rai, komai kankantarsa, amma idan aka ce an sami ragi a yawan mutanen da ake kashewa a kowacce shekara, ni ina ganin abin a yi farin ciki da shi ne.
“Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015, lokacin da Kananan Hukumomi 17 ke karkashin ’yan ta’adda. Hatta NYSC ba ta iya ba matasa masu yi wa kasa hidima horo a wadannan yankunan. Amma a yanzu fa?” in ji shi.