Hukumar NAHCON Ta Gargadi Hukumomin Alhazai Na Jihohi Kan Fadar Kudin Kujerar Da Ya Zarta Wanda Ta Ayyana

Tuni dai hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayyana cewa, ana ta tafka ta’azzara ce a bayan da hukumar ta sanar da fara biyan kudin hajjin karshe na shekarar 2023 a daidai lokacin da wasu jihohi ke bayyana farashin da ya sha bamban da wanda aka amince . 

Jihohi da Hukumar sun amince da kuma yadda Gwamnati ta amince.
Don haka, muna gaggawar sake maimaita abubuwa kamar haka:

Da farko dai jimillar kudin Hajji ya kasance wanda Hukumar ta sanar a ranar Juma’a 7 ga Afrilu, 2023 wanda bai kai Naira miliyan uku (N3,000,000) da ya hada da kudin gida na dukkan nau’in Alhazai da ke karkashin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha.

A cewar sanarwar da mataimakin daraktan yada labarai na hukumar NAHCON, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu,  ta ce Yana da kyau a yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da cewa mu yi aiki tare cikin jituwa da kwanciyar hankali da lumana, ta yadda za mu guji duk wani mataki na cin gajiyar Alhazai.

Ta kara da cewa duk da yake ba mu damu da halin kuÉ—aÉ—en wasu Jihohi ba, amma muna hanzarta sake nanata cewa Hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kakabawa Jihohin da suka yi kuskure takunkumi ta hanyar soke lasisin gudanar da aikinta ko kuma janye Kason Aikin Hajji na 2023 nan take.

Har wa yau, NAHCON na kara jaddada kudirinta na kyautata jin dadin alhazanta da kuma tabbatar da cewa suna da kimar kudi ta fuskar farashi da kayayyakin da za su ci a lokacin aikin hajji.
 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki