Yau INEC Za Ta Taron Gaggawa Kan Zaben Adamawa

A yau Talata Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta gudanar ta taron gaggawa da ta kira kan dambarwar sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa da ya tayar da kura.

Daga taron ne za a ji shawarar da INEC ta yanke a game da sakamakon zaben gwamnan, wanda a ranar Lahadi hukumar ta dakatar da tattarawa saboda rikicin da ya dabaibaye shi.


A ranar Litinin hukumar ta dakatar da Kwamishinan Zabe (REC) na Jihar Adamawa, Barista Hudu Yunus Ari, saboda ya yi gaban kansa wajen ayyana Sanata Aisha Dahiru Binani ta Jam’iyyar APC a matsayin zababbiyar gwamna, alhali ba a kammala tattara sakamakon zaben ba.

Lamarin dai ya yamutsa hazo, amma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda yake neman a zaben a Jam’iyyar PDP, ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, domin INEC za ta dauki matakin da ya dace.


Tuni dai Fintiri da PDP da kungiyoyin kare dimokuradiyya suka yi tir da abin da kwamishinan zaben ya yi, inda suka bukaci INEC ta dauki mataki a kan wannan kwamacala.

Rikicin zaben ya dauki sabon salo ne a safiyar Lahadi a yayin da ake tsaka da jiran lokacin da za a karbi sakamakon kananan hukumomi 10 bayan an karasa zaben a ranar Asabar, amma Barista Hudu ya yi riga-malam-masallacin sanar da cewa Binani ta yi nasara.

Amma daga bisani Hedikwatar INEC ta soke ayyanawar da da Hudu ya yi, cewa haramtacce ne, ba shi da tasiri, sannan ba huruminsa ba ne sanar da sakamakon zabe, aikin Jami’in Tattara Sakamakon Zaben, Farfesa Mele Mohammed ne.


Daga nan Hukumar ta ba da umarnin dakatar da tattara sakamakon zaben, sannan ta umarci Hudu da Farfesa Mohammed da wakilan jam’iyyun da suka shiga zaben da sauran masu ruwa da tsaki su bayyana da hedikwatarta da ke Abuja domin lalubo bakin zaren.


An gudanar da karashen zaben ne a ranar 15 ga watan Afrilu, bayan da INEC ta ayyana wanda aka fara gudanarwa a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammalu ba, saboda soke kuri’un wasu rumufanan zabe da aka yi sakamakon aringizon kuri’u da rigingimun da aka samu a lokacin zaben na farko.
AMINIYA 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki