Labari Da Dumiduminsa : Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirinta Na Janye Tallafin Man Fetur

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur a karshen gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan na daga cikin shawarar da majalisar tattalin arzikin kasa ta yanke a zamanta na ranar Alhamis.

Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Misis Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen taron hukumar zaben da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.



Zainab ta bayyana cewa akwai yiyuwar cire tallafin zai fara aiki a watan Yuni saboda dokar masana'antar man fetur, PIA da kuma kasafin kudin 2023 sun ba da tallafi har zuwa watan Yuni, don haka duk wani jinkiri na iya buƙatar gyara PIA da tanadin kasafin kuɗi.

Ministan, ya ce babu wani wa'adi da aka bayar na cire tallafin, kuma gwamnati mai zuwa za ta yanke shawara a kan lokacin da za ta iya yin hakan.

Cikakken labarin zai zo muku nan gaba kadan

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki