Ganawar da ‘yan majalisar wakilan jam’iyyun adawa suka yi a Najeriya sun yi azarɓaɓi - Masana
Masu sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya na ci gaba da tsokaci a kan ganawar da ‘yan majalisar wakilan da suka fito daga bangaren jam’iyyun hamayya suka yi a makon nan.
Ganawar dai ta samu halartar sabbin ‘yan majalisun da kuma wadanda aka sake zaba domin wakiltar jama’arsu a majalisa ta 10 da ake shirin kafawa a watan Yunin 2023.
Farfesa Kamilu Sani Fagge, malami ne a tsangayar siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano, ya shaida wa BBC cewa, irin wannan ganawa rikita-rikitar siya ce kawai.
Ya ce: “ A gaskiya sun yi sauri wajen gudanar da wannan taro, to amma ina ga sun yi kokari ne da ake cewa a tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro domin idan an zo an rantsar da majalisar, kuma ba su yi wani abu da zai kawo rudani ba, to ko shakka babu ba za a yi da su a majalisar ba.”
Ya ce, ya kamata ‘yan majalisar da suka yi wannan taro su sani cewa har yanzu fa akwai sauran zaben ‘yan majalisun da ba a kammala su ba.
Malamin ya ce: “ A ka’idar zabe na majalisar wakilai kafin a ce jam’iyya na da rinjaye, dole sai tana da kujeru guda 180, wato rabin kujeru 360 din da ake da su a majalisar ke nan.”
Ya ce, “ To ko da wadannan ‘yan majalisar da suka fito daga jam’iyyun hamayya sun hade kansu, to ba su yi rinjayen da za a ce sun kafa rinjaye a majalisar ba.”
Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce a yanzu a majalisar wakilan babu jam’iyyar da ke da wakilai 180, don haka za su iya hada gwiwa su yi aiki tare, to amma kuma idan aka yi hakan a gaba za a iya samun matsala musamman idan aka zo batun rabon mukamai.
Ya ce, “ Idan har aka samu matsala a tsakaninsu to ita kanta majalisar da ma mambobinta ba za su ji dadin aiki ba, saboda rarrabuwar kawuna.”
BBC