Kwamitin Abba Gida-Gida Ya Gargadi Kananan Hukumomi Kan Almubazzaranci

 


Kwamitin Karɓar Mulki na Gwamnan Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, ya gargadi shugabannin kananan hukumomi 44 da ke jihar da manyan ma’aikatansu da su guji bari ana amfani da kudaden kananan hukumominsu ta hanyar da ta sabawa doka.

Shugaban Kwamitin, Abdullahi Baffa Bichi ya ce gargadin ya zama dole domin kuwa sabuwar gwamnatin ba za ta lamunci yin almubazzaranci da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano ba.

A cikin wata takarda da Babban Sakataren Watsa labarai na zababben gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, Baffa Bichi ya ce, “Mun sami labari cewa ana shirin amfani da kudaden kananan hukumomi wajen kammala zabuka a inda ba su kammala ba, a wasu kananan hukumomin Jihar Kano, wanda yin hakan ba dai-dai ba ne kuma ya saba wa doka.”

Abdullahi Bafa Bichi ya ce gwamnati mai jiran gado a jihar ba za ta bari a ɗauki kudaden al’umma a yi wa wata jam’iyyar siyasa aiki ba.

AMINIYA

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki