Maniyyata 51,447 Suka Biya Kudin Hajin 2024 - NAHCON
Bayan rufe biyan kudin Hajji, adadin maniyyatan da suka yi rijistar zuwa aikin hajjin 2024 daga Najeriya ya kai 51,447 a karkashin kason gwamnati.
A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da jama'a ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace abin yabawa ne, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta taka rawar gani wajen ganin an cimma wannan kyakkyawar manufa.
Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta amince da sadaukarwa da dama da gwamnatin tarayya ta yi a kan duk wata matsala da ta taso wajen ganin an samu saukin matsalolin da ke addabar maniyyata.
Hukumar ta kuma yaba da hakurin da mahajjata suka nuna a cikin rashin tabbas.
Damuwar da Malamai suka nuna kan halin da Alhazai ke ciki bai wuce Hukumar ta lura da shi ba. Masu ruwa da tsaki da dama, ciki har da Gwamnonin Jihohi, sun ba da mafita daga halin da aka tsinci kai.
Wasu kafafen yada labarai sun nuna matukar fahimtar matsalolin da a zahiri suka fallasa gaskiyar lamarin da Hajjin 2024 ke fuskanta.
Hakika shirye-shiryen Hajjin 2024 ya zo da kalubalen da ba a zata ba wanda daga ciki aka koyo darussa.
NAHCON dai ta san cewa tsare-tsare na dogon lokaci shi ne dabarun da za a iya aiwatar da su da za su shawo kan kalubalen da suka kawo tsaiko a shirye-shiryen Hajjin bana.
A ci gaba, tsare-tsare na dogon lokaci shi ne tsarin da Hukumar za ta bi wajen gudanar da ayyukanta kafin aikin Hajji.
Haqiqa ta tabbata cewa dukkan masu ruwa da tsaki a aikin Hajji dole ne su hada hannu domin kaucewa kalubalen da ba a zata ba.
Jadawalin dake kasa dai na daga cikin adadin maniyyatan da suka yi nasarar yin rijistar aikin Hajjin 2024 daga kowace jiha.
S/N
Jiha
Jimillar adadin mahajjatan da suka yi rajista
1
Adamawa
1,642
2
Borno
1,780
3
Taraba
950
4
Yobe
1,120
Maid./Yola Sub- jimlar
5,492
5
Bauchi |
2,315
6
Binuwai
87
7
Ekiti
186
8
FCT
2,491
9
Gombe
1,373
10
Jigawa
1,250
11
Kaduna
4,493
12
Kano
3,057
13
Katsina
2,654
14
Kebbi
3,419
15
Kogi
13
16
17
Kwara
Nasarawa
3,000
1,866
18
Nijar
3,201
19
Ondo
491
20
Plateau
1 126
21
Sokoto
3,643
22
Zamfara
1,596
Jumlar Arewa
36,261
23
Abiya
-
24
Akwa-Ibom
-
25
Anambara
-
26
Bayelsa
13
27
Cross River
-
28
Delta
36
29
Ebonyi
13
30
Edo
295
31
Enugu
18
32
Imo
100
33
Legas
1 861
34
Ogun
925
35
Osun
1,590
36
37
Oyo
Rivers
1,047
47
38
Sojojin Kasar
365
Kudancin Jumla
6,310
JAMA'A DAGA JIHOHI
48,063
39
HSS
1884
40
Wasu
1,500
JIMILLAR YAWANSU
51,447