Gwamnan Kano Ya Bayar Da Kyautar Kujerar Hajji Ga Matashin Da Ya Samu Nasara A Gasar Haddar Alkur'ani
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nuna na karramawa tare da tallafawa masu hazaka na musamman a cikin jihar ta hanyar ba da kyautar kujerar aikin Hajji ga wani babban matashi.
A wani biki da aka gudanar a ofishinsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda Darakta na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya wakilta, ya sanar da basa kyautar kujerar Hajji ga Sheikh Ja’afar Habib Yusuf mai shekaru 16
Hazakar Sheikh Ja'afar Habib Yusuf ta burge zukata da tunani ta hanyar haddar Alkur'ani mai girma da zurfin sanin abin da ke cikinsa. Musamman ma, yana da kyakkyawar fahimta ta kowace aya da inda take a cikin littafi mai tsarki, yana nuna sadaukarwa mara misaltuwa ga ban gaskiyarsa da koyarwarta.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa Sheikh Ja'afar bisa jajircewarsa da kuma ilimin Alkur'ani, inda ya bayyana shi a matsayin misali na hasken addini a jihar Kano.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin renon matasa masu basira irin su Sheikh Ja'afar wadanda ke wakiltar shugabanni da jakadun jihar nan gaba.
Bayar da kyautar kujerar aikin Hajji ga Sheikh Ja'afar Habib Yusuf wanda ya fito daga Goron-Dutse a karamar hukumar Dala, ya zama alama ce ta karramawa da kuma jinjinawa irin nasarorin da ya samu a karatun Alkur'ani da kuma jajircewarsa na neman wayewar kai.
Gwamnatin jihar Kano dai na ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen ganin ta inganta hazaka a kowane fanni, sannan ta yi alkawarin ci gaba da bayar da goyon baya ga shirye-shiryen da za su karfafa da kuma daukaka matasan jihar.