Gwamna Abba Kabir Yayi Ta'aziyyar Rasuwar Marigayi Dr. Faizu Baffa Yola

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar Dakta Faizu Baffa Yola wanda ya rasu a yau (Alhamis) sakamakon rashin lafiya da ya yi yana da shekaru 74 a duniya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana a cikin wani yanayi na alhini game da gudunmawar da Marigayi Dokta Faizu Baffa Yola ya bayar wajen ci gaban harkokin kiwon lafiya a jihar da kuma wajensa da kuma yadda yake taimakawa bil’adama a kowane lokaci.

“Mun samu matukar kaduwa da labarin rasuwar Dr. Faizu Baffa Yola, wani kwararren likita wanda ya shafe tsawon rayuwarsa yana hidima ga al'uma a fannin kula da lafiya da sauran ayyukan jin kai.

“Abubuwan alkhairin da ya yi ba zai gushe ba saboda gudunmuwar da ya bayar a ci gaban jihar da kasa baki daya ba za a iya mantawa da shi cikin sauki ba kuma zai zama jagora ga masu son bin tafarki madaidaici.

“A madadin gwamnati da na al’ummar jihar nan, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalansa da al’ummar jihar, tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya yafe masa ya kuma sa Aljannar Firdausi ta kasance a gidansa na karshe.” Gwamnan yayi addu'a 

Marigayi Dokta Faizu Baffa Yola ya kasance gogaggen Likita wanda ya ke aikin sirri kafin a nada shi kwamishinan lafiya a jihar Kano a zamanin marigayi Kanar Muhammad Abdullahi Wase.

An kuma nada shi Kwamishinan Albarkatun Ruwa a Kano a zamanin Marigayi Birgediya Janar Dominic Obukadata Oneya.

Ya shiga siyasar bangaranci kuma a lokaci daya ya tsaya takarar Sanatan Kano ta tsakiya a karkashin rusasshiyar jam’iyyar Republican Convention (NRC).

Ya rasu ya bar matarsa da ’yan’uwansa da ’yan uwa da dama ciki har da tsohon Kwamishinan Karkara da Raya Al’umma Dr. Mahmoud Baffa Yola, tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, Hon. Abdurraman Baffa Yola da Ismail Garba Yola, Manaja a daya daga cikin reshen bankin First Bank da ke Kano.

Dr. Fa'izu Baffa shi ne likita na 5 dan asalin jihar Kano da ya yi aiki a Kano kuma ya ci gaba da aikin jinya da tiyata har ya rasu.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki