Damuwata Game Da Al'ummata Ta Musulmin Arewa Kullum Karuwa Take - Farfesa Salisu Shehu
Hankalina na ci gaba da tashi duk lokacin da na yi tinani gameda tabarbarewar iliminmu, alhali kuma ba a ma kama hanyar gyara ba.
Hankalina na ci gaba da tashi saboda gamsuwa da na yi cewa tozarta 'ya'yan talakawa da jahilci da 'ya'yan talakawa 'yan uwansu suka yi, shi ne ummul khaba'isin yaduwar ayyukan laifi kamar su daba, jagaliya, sara-suka, fashi da makami, kidnapping, da sauransu.
Tabbas, 'ya'yan talakawa, wadanda aka ilmantar da su FREE, kuma cikin cikakkiyar kulawa da gata, su ne yanzu suke madafun iko, su ne manyan civil servants, public office holders (shugabannin Gwamnati), wadanda suka mai da dukiyar Gwamnati ganima, suke wabtarta (satarta) gaba gadi, su ne suka rusa iliminmu, kuma suke hana 'ya'yan talakawa samun ingantaccen ilimi.
Wanda duk ya ji labarin yanda Musulmin Arewa suka yi barin dollars ( daloli) a Saudiyya, a Umurar Ramadan bana, tun daga hamshakan hotels na kusa da Harami, wadanda kusan duk mutanenmu ne suka kakkamesu, suka kankanesu, zuwa ga kashe-kashen kudi na FITAR hankali, dole takaici ya damu duk wanda ke da damuwa da makomar iliminmu.
Zuciyata tana kara cika da takaici, idan na tina cewa, 'ya'yan talakawa irina, masu shekaru kamar nawa KO Sama da ni a shekaru , wadanda yanzu muka hana 'ya'yan talakawa 'yan uwanmu ilimi, abincin da ake ciyar da mu a makarantin boarding na sakandare har zuwa jami'ah, WALLAHI bama cin irin wannan abincin a gidajen iyayenmu. Kuma na kalubalanci duk wanda ya yi sakandare KO Jami'ah a shekarun 1970s zuwa early 1980s ya karyata wannan maganar da na yi.
Hankalina na kara tashi idan na yi nazarin alkaluman adadin malamai a makarantunmu na primary da sakandare a Jihohin Musulmi na Arewa. A mafiya yawan Jihohin Arewa babu isassun Malamai a makarntun da suke kauyuka. Kuma akwai yara da suka yi digiri birjik amma ba a daukarsu aiki. Malamai suna mutuwa, da yawa kuma suna ritaya, amma ba a cike gurabansu. A irin wannan yanayin ne kuma za ka ga 'ya'yan talakawan da aka ilmantar da su a wadannan makarantun Gwamnati na kauyukan suna fantamawa su da 'ya'yansu cikin wani irin salon rayuwa na almubazzaranci, da barna, sharholiya, da hululu da alfahari da dai sauran munanan halaye na barnar da take alamta mugunta da keta da rashin tausayawa GA talakawa.
Wata karya da ake ta raina hankali da rashin kunya ita ce cewa da ake wai ai babu kudi ne a Kasa. KO kuma wai yanzu dambu be ya yi yawa baya Jin mai.. Amma wannan bai taba hanasu rayuwar almuzzaranci da israfi da suke yi da dukiyar al'umma BA. Idan Ka kusancesu, ka ga yanda suke wadaka da dukiyar al'umma KO kaga tsari na rayuwarsu da iyalansu (life style dinsu) ba za ka taba zaton akwai matsaloli a rayuwar al'ummarmu BA.
Hankalina na tashi idan na lura cewa, akasarin malamanmu hankalinsu baya kaiwa ga hango hatsarin da muke fuskanta a dalilin tabarbarewar iliminmu, balle su rika yawaita fadakarwa akai.
Yanzu makarnatunmu na Gwamnati sun zama kufai. Musamman wadanda ba state capital suke ba. Sun zama kufai alal hakika, Kai Ka CE ragowar yaki ne. Idan na ga makarantun nan, sai na tina wadansu 'yan baitoci na Infiraji, inda Malam Aliyu Namangi, rahimahullahu yake cewa:
"IDAN NA RATSA KUFAI ZUBABBE,
SAI NA KAN TINA YAU DA GOBE,
DA MUTANE TAI WA ZOBE,
YAU GA SARKI DA BABE,
TA CIKASU DA KWANSUNAN MAHARBA,
DA GURIN SAI MASU IKO,
YANZU BA KO MASU TARKO,
SAI FA RIMAYE DA BOKKO,
TO FA MAI SON NUNA IKO,
BA AKAI GA I SU A MALLAKA BA.
DANDALINSU NA CIN ABINCI,
BABU KOWA SAI KUMURCI,
DAKUNANSU DILA KA BARCI,
DA TANA DA RIKON AMINCI, BAWA JANGWARZO BA YA MACE BA".
Abu ne mai sauki Ka ji cewa a jiha guda an kashe rabin biliyan KO biliyan wajen tura mutane umura. Mafiya yawan wadanda ake turawa malamai ne, wadanda wadansu daga cikinsu sun je umura kamar sau ashirin KO fiye da haka. Ina ma da Malaman nan za su iya hakura su hada kansu su ce da Gwamna, mun jejje umuran nan, wadannan madudun kudade a sarrafasu wajen gyara iliminmu. Da za a iya samun haka, Wallahi da za mu ga canji mai kyau a makarantunmu na Gwamnati.
Dole ne hankalina ya rika tashi duk lokacin da na tina cewa makomarmu a matsayin Al'umma BA za ta yi kyau ba matikar bamu shiga hankalinmu da taitayinmu mun gyara tsarin iliminmu BA.
A dai dai wannan gaba nake tina baitocin Malam Sa'adu Zungur, rahimahullahu. Wadanda a cikinsu yake bayyana takaicinsa shi ma dangane da yanda muka yi watsi da al'amarin ilimi. Yana cewa'
"Shehu Abdullahi hakikatan ya bar mana Gadon gaskiya
Ilimi, hikima addini duka, da dabarar sarrafa Duniya
Muka lalata, muka wargaza, gashi yau ana mana dariya,
Jahilci ya ci lakarmu duk, ya sa mana sarka har wuya,
Ya sa mana ankwa hannuwa, ya daure kafarmu d tsarkiya
Bakunanmu ya sa takunkumi, BA zalaka sai sharholiya
Ilimi mai amfani duka,inda addininmu ya dogara,
In fa addini ya raunana, babu alheri nan duniya".
A can gaba, Malam Sa'adu Zungur ya ce:
"Mu dai ilimi muka tambaya, KO a London ko a Arebiya"..
A can gaba, bayan Malam Sa'adu Zungur ya kara zayyana wadansu illolin al'ummarmu, inda ya ke cewa:
"matikar 'yan iska na gari, Dan Daudu d shi da magajiya,
Da samari masu ruwan kudi, da maroka can a gidan giya ,
Matikar da musakai barkatai, da makaho KO da makauniya,
Matikar yaranmu suna bara, Allah baku mu samu abin miya,
A gidan birni da na kauyuka, babu mai tanyonsu a Hausa duk, babu shakka sai mun sha wuya.
A Arewa zumunta ta mutum, sai karya sai kwambon tsiya,
Sai alfahari da yawan kwafa, GA hula mai annakiya,
Gorin asali da na dukiya sai Ka CE Dan annabi FARIYA.
Kai Bahaushe bashi da zuciya, Zai sha kunya nan duniya".
A karshen dai Malam Sa'adu Zungur ya ce,
"WAGGA AL'UMMA ME ZA TA WO? A CIKIN ZARAFOFIN DUNIYA?
Wadannan gwalagwalan baitoci Malam Sa'adu Zungur ya yisu ne sama da shekara HAMSIN (50).
Amma me ya canja dangane da lamrinmu in banda karin lalacewar ilimi da tabarbarewarsa?
Idan muka sake komawa wajen Malam Sa'adu Zungur, sai mu rufe wannan tanbihi da wani baitin nashi inda yake cewa:
".MU DAI HAKKINMU GAYA MUKU, KO KU KARBA KO KU YI DARIYA ,
DARIYARKU TA ZAN KUKA GABA, DA NADAMAR MAI KIN GASKIYA".
Amma a karshen karshe, wajibi ne mu koma SHA KUNDUM, KANKAT, GAGARABADAU, AL'QUR'ANI, GAGARA GASA:
Cikin Suratul Isra'i, Allah cewa Ya yi:
{ وَإِذَاۤ أَرَدۡنَاۤ أَن نُّهۡلِكَ قَرۡیَةً أَمَرۡنَا مُتۡرَفِیهَا فَفَسَقُوا۟ فِیهَا فَحَقَّ عَلَیۡهَا ٱلۡقَوۡلُ فَدَمَّرۡنَـٰهَا تَدۡمِیرࣰا }
[Surah Al-Isrāʾ: 16]
Cikin Suratul An'am, Allah cewa Ya yi:
{ وَكَذَ ٰلِكَ جَعَلۡنَا فِی كُلِّ قَرۡیَةٍ أَكَـٰبِرَ مُجۡرِمِیهَا لِیَمۡكُرُوا۟ فِیهَاۖ وَمَا یَمۡكُرُونَ إِلَّا بِأَنفُسِهِمۡ وَمَا یَشۡعُرُونَ }
[Surah Al-Anʿām: 123]
Cikin Suratul Hud, Allah Ya ce:
{ فَلَوۡلَا كَانَ مِنَ ٱلۡقُرُونِ مِن قَبۡلِكُمۡ أُو۟لُوا۟ بَقِیَّةࣲ یَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡفَسَادِ فِی ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا قَلِیلࣰا مِّمَّنۡ أَنجَیۡنَا مِنۡهُمۡۗ وَٱتَّبَعَ ٱلَّذِینَ ظَلَمُوا۟ مَاۤ أُتۡرِفُوا۟ فِیهِ وَكَانُوا۟ مُجۡرِمِینَ }
[Surah Hūd: 116]
Cikin Suratul Ma'idah,Allah Ya ce:
{ وَتَرَىٰ كَثِیرࣰا مِّنۡهُمۡ یُسَـٰرِعُونَ فِی ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَ ٰنِ وَأَكۡلِهِمُ ٱلسُّحۡتَۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُوا۟ یَعۡمَلُونَ (62) لَوۡلَا یَنۡهَىٰهُمُ ٱلرَّبَّـٰنِیُّونَ وَٱلۡأَحۡبَارُ عَن قَوۡلِهِمُ ٱلۡإِثۡمَ وَأَكۡلِهِمُ ٱلسُّحۡتَۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُوا۟ یَصۡنَعُونَ (63) }
[Surah Al-Māʾidah: 62-63]
{ لُعِنَ ٱلَّذِینَ كَفَرُوا۟ مِنۢ بَنِیۤ إِسۡرَ ٰۤءِیلَ عَلَىٰ لِسَانِ دَاوُۥدَ وَعِیسَى ٱبۡنِ مَرۡیَمَۚ ذَ ٰلِكَ بِمَا عَصَوا۟ وَّكَانُوا۟ یَعۡتَدُونَ (78) كَانُوا۟ لَا یَتَنَاهَوۡنَ عَن مُّنكَرࣲ فَعَلُوهُۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُوا۟ یَفۡعَلُونَ (79) }
[Surah Al-Māʾidah: 78-79]
{ قُل لَّا یَسۡتَوِی ٱلۡخَبِیثُ وَٱلطَّیِّبُ وَلَوۡ أَعۡجَبَكَ كَثۡرَةُ ٱلۡخَبِیثِۚ فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ یَـٰۤأُو۟لِی ٱلۡأَلۡبَـٰبِ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ }
[Surah Al-Māʾidah: 100]
ALLAH YA BAMU IKON GYARAWA CIKIN SAUKI.