Nan Ba Da Jimawa Ba Matsalar Ruwa Za Ta Zama Tarihi A Kano - Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano ta ce tana bakin kokarinta wajen ganin ta shawo kan matsalar karancin ruwan sha a birnin Kano da kewaye.

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Dr Ali Haruna Makoda ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Kano ranar Laraba.

“Muna aiki tukuru domin ganin mun gyara matsalar karancin ruwan sha a babban birnin jihar da kewaye, kuma nan ba da jimawa ba za a kawo karshen matsalar,” inji Makoda.


Ya dora alhakin kalubalen a kan cikakken kayan aiki, musamman a cibiyar kula da ruwa ta Tamburawa da ke samar da ruwa ga mafi yawan sassan birnin Kano.

Ya ce tsananin zafin da ake fuskanta a yankin shi ma ya jawo matsalar karancin ruwan, yayin da mutane ke amfani da ruwa mai yawa don jure yanayin.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta gaji lalacewar sha’anin ruwa daga gwamnatin da ta shude wanda ba ta ba da kulawar da ya kamata ba wajen samar da ruwan sha.

A lokacin gwamnatin da ta shude, kwamishinan ya ce kashi 20 cikin 100 na bukatun ruwan jihar ne kawai ake samar da su, wanda a cewarsa bai wadatar ba.

“Amma yayin da muka shiga ofis, gwamnatinmu ta iya samar da sama da kashi 60 na bukatun ruwan al’ummarmu,” inji shi.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar na kashe naira biliyan 1.2 duk wata domin inganta samar da ruwan sha a yankin.


Irin wadannan kashe-kashen inji Makoda, sun hada da siyan man dizal akan kudi naira miliyan 400, da kuma naira miliyan 387 wajen siyan sinadarai da kuma biyan kudin wutan lantarki har naira miliyan 280 duk wata.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta kulla yarjejeniya da gwamnatin Faransa kan kashe kudi Euro miliyan 63.4 domin gina kamfanin sarrafa ruwa na Kano karo na uku.

“Mun jajirce sosai wajen ganin an samu isasshen ruwan sha a Kano, dalilin da ya sa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke yin duk abin da za ta iya, ciki har da kashe dimbin albarkatu domin samar da isasshen ruwan sha a cikin tsohon birnin da kewaye.” Kwamishinan ya kara da cewa.
(Bizpoint)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki