Sama da mutum 1,000 'Yan APC Sun Koma Jam'iyyar NNPP
A wani gagarumin sauyi sama da mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 1,000 na jihar Kano suka sauya sheka zuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a ranar Asabar.
Mutanen sun fito ne daga kananan hukumomin Shanono da Bagwai, mataimakin gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo a madadin gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya tarbe su a fadar gwamnatin jihar Kano.
Wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu ya rabawa manema labarai, ya bayyana jin dadin Gwarzo na karbar wadanda suka sauya sheka. Ya jaddada cewa jam’iyyar NNPP ta ba da fifiko kan hadin kai kuma za a yi wa daukacin mambobinsu adalcin da ya dace.
A cewar Garba, mataimakin Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin na aiwatar da shirye-shiryen da za su amfani daukacin jihar Kano, ya kuma bukaci a ci gaba da baiwa gwamnati goyon baya domin ci gaban jihar.
Da yake jawabi tun da farko, shugaban masu sauya shekar, Alhaji Haruna Babangida Abbas (Kosashe), ya bayar da misali da halayya da salon mulkin Gwamna Abba a matsayin dalilan da suka sa suka yi wannan yunkuri.
Ya kuma bayyana nadamarsu ga jam’iyyar APC a baya, ya kuma yi alkawarin yin aiki da jam’iyyar NNPP domin ci gaban Kano.
Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban NNPP na Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa ya yi maraba da sabbin mambobin tare da bada tabbacin shiga harkokin jam’iyyar.
Ya kuma ja hankalin ‘ya’yan sauran jam’iyyu ciki har da APC da su shiga jam’iyyar NNPP domin ci gaban jihar.
Dungurawa ya kuma bukaci tallafawa shirye-shirye da manufofin gwamnati.
Taron ya samu halartar manyan mutane kamar kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar Kano, Alhaji Musa Suleiman Shanono, da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP da dama wadanda suka yi murnar shigowar sabbin mambobi.