Search This Blog

Thursday, 4 April 2024

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Kano Ta Shigar Da Karar Tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, Matarsa, Hafsat Wasu Mutane 6 A Kotu Akan Zargin Cin Hanci Da Rashawa

Gwamnatin jihar Kano ta shigar da karar tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat Umar, Umar Abdullahi Umar da wasu mutane biyar a gaban kotu bisa zarge-zarge 8 da suka hada da cin hanci da rashawa da karkatar da wasu kudade da suka shafi biliyoyin naira.



Wannan yana kunshe ne a cikin takardar tuhuma mai kwanan wata 3 ga Afrilu, 2024 tare da jerin shaidu 15 da aka makala.



SOLACEBASE ta ruwaito cewa sauran wadanda ake kara a karar sun hada da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises.

, Cikakken labarin zai zo muku nan gaba kadan 

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Head of Service Urges Civil Servants to Uphold Ethical Conduct

The Head of Service, Kano State, has called on civil servants to strictly adhere to the Civil Service ethical code and show grea...