DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta tabbatar da dakatar da Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC

Wata babbar kotu a jihar Kano ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

A tuna cewa a kwanaki biyu da suka gabata ne shugabancin APC na mazabar Ganduje a Karamar Hukumar Dawakin Tofa, mahaifar Ganduje, ya dakatar da shi bisa zargin cin-hanci da rashawa da gwamnatin Kano ke yi masa.

A wata ƙwarya-ƙwaryar umarni, kotun, ƙarƙashin Mai Shari’a Usman Na’abba, ta hana Ganduje, wanda shine tsohon gwamnan Kano, nuna kan sa a matsayin shugaban jam’iyyar APC.

Na’abba ya kuma hana Ganduje yin wani taro ko daukar mataki a matsayin shugaban jam’iyyar har sai an kammala zaman sauraron karar.

Ya kuma hana shugabancin jam’iyyar na jiha shiga cikin maganar da take gaban kotu.

Dr. Ibrahim Sa’ad, a madadin biyu daga cikin shugabannin APC na mazabar Ganduje, mataimakin sakatare, Laminu Sani da mai baiwa jam’iyyar shawara kan harkokin Shari’a, Haladu Gwanjo ne ya shigar da karar.

Haka kuma kotun ta umarci waɗanda ake kara su hudu da suka haɗa da jam’iyar APC a matakin kasa da jiha da kuma shi Ganduje din da su tsaya a matsayin su daga 15 ga Afrilu zuwa 30 ga watan Afrilu lokacin da za a saurari karar.

(Daily Nigeria Hausa)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki