Ba Zamu Lamunci Yi Mana Katsalandan A Ayyukanmu Ba - EFCC

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta yi kira ga jama’a  cewa laifi ne a hana jami’an hukumar gudanar da ayyukansu na halal.

A sanarwar da Shugaban sashen hulda da jama'a na hukumar, Dele Oyewale ya sanyawa hannu, yace Sashi na 38(2)(a(b) na dokar kafa hukumar EFCC ya sanya laifin hana jami'an hukumar gudanar da ayyukansu na halal. Masu laifi suna fuskantar daurin kurkuku na kasa da shekaru biyar.

Wannan gargadin ya zama dole bisa ga yadda mutane da kungiyoyin da Hukumar ke bincike ke kara ta'azzara na daukar doka a hannunsu ta hanyar daukar 'yan baranda domin dakile ayyukan EFCC.

A lokuta da dama, jami’an Hukumar sun yi taka-tsan-tsan wajen tunkarar irin wannan tada zaune tsaye domin gujewa tabarbarewar doka da oda. Abin takaici, ana É—aukar irin wannan halin a matsayin alamar rauni.

Don haka hukumar ta yi gargadin cewa daga yanzu ba za ta lamunci duk wani yunkurin wani mutum ko kungiya na kawo cikas ga ayyukanta ba domin kuwa za a fuskanci hukuncin da ya dace.



Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki