Fiqhun Aikin Hajji: Matsayin Izinin Miji ga Matarsa


✍️ Mansur Sokoto

An tambayi Sheikh Muhammad bn Saleh Al-Uthaimin (rh): Idan namiji ya hana matarsa zuwa aikin Hajji ko yana da zunubi?

Sai ya amsa da cewa: "Eh, yana da zunubi kam in har ya hana ta zuwa Hajji alhalin sharuɗɗan Hajjin sun cika. Yana da laifi. Ina nufin idan misali ta ce masa, ga ɗan uwana zai tafi da ni aikin Hajji kuma ina da guzuri ba ni buƙatar ka ƙara mani kome, alhalin ba ta sauke farali ba. Ya wajaba ya yi mata izini. In kuma bai yi ba za ta iya yin Hajjinta ko ba da izininsa ba, sai fa in tana jin tsoron ya sake ta. A nan kam tana da uzuri". "Al-Fatawa" na Ibnu Uthaimin (21/115).

Fiqhun Wannan Fatawa:
1. Aikin Hajji yana da sharuɗɗa. Amma idan na farilla ne izinin miji ba ya cikin sharuɗɗan.
2. Ko da Hajjin farilla ne, ana buƙatar izininsa domin girman haƙƙensa da yake wajibi a kan ta. Idan ta tafi Hajji haƙƙoƙinsa da yawa za su faɗi.
3. Idan Macce ta samu dalilin yin Hajjin farilla wajibi ne Mijinta ya yi mata izini sai idan akwai wani dalili mai ƙarfi saboda haƙƙen Allah yana gaba ga nasa.
4. Idan Macce za ta yi Hajji bayan ta sauke farali wajibi ne ta samu izinin mijinta. Idan bai yi izini ba sai ta yi haƙuri ta wadatu da wasu ibadun ko kuma ta biya ma wani ya yi mata aikin Hajjin.
5. Idan an biya ma Macce kujerar Hajji tare da mijinta, a nan ya fi zama wajibi ya amince da tafiyarta, saboda idan suna tare da yawan haƙƙoƙinsa a kan ta ba su faɗuwa. 
6. Haƙƙen Allah yana gaba da na kowa har da miji (da iyaye). Don haka macce za ta iya yin aikin Hajjin farali tare da iyayenta ko yayyenta/ƙannenta ba da izinin mijinta ba idan an neme shi izinin ya ƙiya.
7. Wajabcin aikin Hajji na gaggawa ne ko yana da jinkiri?
Misali, idan mutum ya samu sukuni da halin zuwa Hajji a bana, wajibi ne ya yi Hajji a wannan shekarar? Ko zai iya yin jinkiri sai wata shekara ko wasu shekaru masu zuwa? Ra'ayoyi biyu ne na Malamai.
Ra'ayin farko shi ne na Imam Abu Hanifa da Imam Malik (rh) saboda rayuwa ba ta da tabbas, haka ma lafiya da samun iko suna iya kuɓucewa.
Ra'ayi na biyu shi ne na Imam As-Shafi'i (rh), saboda Manzon Allah (S) bai yi Hajji ba a shekara ta tara - alhalin an wajabta Hajji kuma an buɗe birnin Makka tun a shekara ta takwas, haka ma mafi yawan Musulmi ba su je Hajji a wannan shekarar ba, sai dai kawai Manzon Allah (S) ya wakilta sayyidina Abubakar (ra) da wasu daga cikin Musulmi suka tafi. Idan mutum ya samu ikon Hajji bana amma bai tafi ba, in ya je baɗi ba a cewa ramko ne ya yi. Don haka daman wajibin ba na gaggawa ba ne, in ji Imam Shafi'i (rh).
Bisa ga wannan fahimta ta biyu, miji na iya hana matarsa tafiya Hajjin farilla don ta jira har ya kimtsa ya samu halin tafiya tare da ita.
8. Maslahar auren Macce tana gaba da sauke faralin Hajji da gaggawa. Don haka, idan saɓa ma mijinta ta tafi aikin Hajji - ko da na farilla ne - zai iya janyo mata zawarci, za a ba ta shawarar ta saurara har ta samu izininsa a nan gaba. 
9. Yau da gobe ta nuna mana haɗurran da ke tattare da Hajjin Macce babu tsayayyen namiji tare da ita (akwai abubuwan da suka sha faruwa a birnin Makka waɗanda muka shaida kuma ba su da daɗi). Bisa ga haka, kuma gini a kan fahimtar Imam As-Shafi'i babu laifi miji ya jinkirta tafiyar matarsa bayan an biya mata kujera da zimmar su tafi tare misali a wata shekera.
10. Yana da kyau wanda zai biya ma Matar wani kujerar Hajji ko Umra - ko da mahaifinta ne ko ɗan uwanta - ya fara tuntuɓar mijinta don samar da maslaha da hana yamutsewar hazo. Idan kuma akwai hali sai a biya masu tare saboda kyautatawa da kuma kauce ma fitina.
11. Wani yakan hana matarsa zuwa aikin Hajji - ko da iyayenta ko yan uwanta sun biya mata saboda kishiyarta ba ta samu zuwa ba. Wannan ba uzuri ba ne, kuma da wannan dalili ba ya halalta ya hana mata sauke faralinta.

Cikakken sani yana wurin Allah maɗaukakin Sarki.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki