Shugaban NAHCON Ya Yabawa Gwamnan Imo Bisa Tallafawa Maniyyatan Jahar

Hukumar alhazai ta kasa NAHCON a yau ta karbi bakuncin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda ya kai ziyarar ban girma a gidan alhazai dake Abuja.

A sanarwar da mataimakin daraktan yada labarai na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace A jawabinsa na maraba, Malam Jalal Ahmad Arabi ya bayyana jin dadinsa da karbar bakuncin Gwamnan Jihar Imo a gidan Hajji.

Arabi ya bayyana Gwamna Uzodinma a matsayin wani ginshikin tallafi ga Hukumar tare da bayyana yadda ya yi kokarin ganin alhazan jihar sa da ke da niyyar shiga aikin Hajjin bana.

A cewarsa, “Kun kasance ginshikin goyon bayanmu a Hukumar ta hanyar goyon bayanku na ganin cewa Musulmin Jihar Imo sun samu damar shiga aikin Hajji. Kun tallafa mana a 2023 da ma bana duk da kasancewar kiristanci ne kuma jihar Imo jihar ce mafi rinjayen Kirista. A gare mu ku alama ce ta zaman lafiya tare da addini da hadin kai a kasar."

Ya kuma baiwa Gwamna Hope Uzodinma takardar yabo da lambar yabo ta 🥈 f nagari bisa goyon bayansa da inganta zaman lafiya da hadin kan addini.

A nasa martanin, Gwamna Uzodinma ya bayyana matukar jin dadinsa da karramawar da aka yi masa tare da jaddada imaninsa na ganin an zaunar da juna cikin lumana domin bunkasa ci gaba da wadata a jihar Imo da Najeriya baki daya.

Idan dai za a iya tunawa, Gwamnan na daya daga cikin gwamnonin kalilan da suka bayar da tallafi dangane da aikin Hajjin 2024 wanda ya baiwa alhazan jiharsa da ke da niyyar shiga aikin Hajjin bana.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki