Search This Blog

Monday, 27 May 2024

Yanzu-Yanzu: Muhimmiyar Sanarwa Daga Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Kano

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, karkashin Jagorancin Alh, Lamin Rabi'u Danbappa, na sanar da Maniyyatan Da suka fito daga  Kananan hukumomin

 1:- Gwarzo 
 2:- Karaye
 3:- Kiru
 4:- Shanono
 5:- Rogo 
 6:-Dawakin Tofa
 7:-Bagwai
 8:-Bichi
 9:-Ghari
 10:-Tsanyawa
  11:- Wudil da Kuma Karamar Hukumar 
  12:- Gaya.

Dasu fito zuwa Sansanin Alhazai na Jiha a Gobe Talata 28-05-2024 da misalin karfe tara na safe 9:00 Domin tantancesu zuwa kasa mai tsarki.

      Maniyyatan zasu fito da manya da Kananan jakankunan su tare da tabbatar wa cewa Basu saka komai a cikin Babbar jakar ba.

  Allah ya bada ikon fitowa cikin koshin lafiya 

       Sanarwa daga
Sulaiman Abdullahi Dederi
Jami'in Yada Labarai da Hulda da jama'a na hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...