Hajj2024: Hukumar Alhazai Ta Jahar Kano Ta Bukaci Alhazai Da Su Guji Ficewa Daga Rukunin Da Aka Sanyasu

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya sake jaddada a yau muhimmancin alhazai wajen bin tsarin kungiya a yayin da ake ci gaba da gudanar da horaswa na yau da kullum a Cibiyar Musulunci ta Rano.

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya jaddada cewa rukunin ko kuma kumgiya wani sabon umarni ne daga Hukumar Alhazai ta Saudiyya, wanda ke bukatar kungiyoyin mutane arba’in da biyar karkashin jagorancin mace daya namiji da daya.
Ya kara jaddada wajabcin bin wadannan umarni na tashi daga Jidda har zuwa kammala aikin Hajji.

Dangane da kudin guzuri  (BTA), ya bukaci alhazai da su guji sayayyar da ba dole ba, yana mai bayyana cewa, manufar wannan kudi shi ne biyan bukatar da ba zato ba tsammani ko na gaggawa.
Alhaji Lamin Rabi’u, wanda ya samu wakilcin mamban hukumar kuma shugaban Kwamitin Malaman Bita na jihar, Sheikh Tijjani Sani Maihula, ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar Kano ta samar da abinci, magunguna, dakunan kwana, da sufuri, tare da kawar da bukatar karin kashe kudade.

Bugu da kari, Daraktan ayyukan Hajji Alhaji Kabiru Muhd ​​Panda wanda mataimakinsa Alhaji Muktar Muktar ya wakilta ya bayyana cewa sun ziyarci cibiyar ne domin ganin an duba lafiyar dukkan alhazai don gudun kada a bar kowa a baya.
Yankunan da aka ziyarta sun hada da kananan hukumomin Rano, Kibiya, da Bunkure, bi da bi.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki