Kuna Da Rawar Takawa Wajen Gudanar da Harkokin Filaye - Kwamishinan Kasa Ga Kwamitin Majalisa Kan Filaye

Kwamishinan kasa da tsare-tsare na Jiha, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ya yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da kwamitin majalisar dokokin jihar kan filaye domin inganta harkar filaye a jihar.

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar, Murtala Shehu Umar ya sanyawa hannu, yace Kwamishinan ya bayyana haka ne a yau (Juma’a) a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban da mambobin kwamitin majalisar dokokin jihar a kan filaye a ofishinsa.

 Ya ce tun da ya hau kan karagar Shugabanci  ya ci gaba da yin aiki don gyara matsaloli da kalubalen da ke gaban ma’aikatar da kuma kawo cikas ga gudanar da harkokin mulki mai inganci a jihar.
Don haka ya yi kira gare su da su ba shi goyon baya da hadin kai a kan hakan domin a matsayinsu na mambobin kwamitin kula da filaye suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen gyara harkokin mulki.

Kwamishinan ya sanar da kwamitin cewa ma’aikatar na da kwararrun daraktoci kuma sun yi alkawarin ba shi dukkan goyon bayan da ake bukata.
Ya kuma tabbatar wa da kwamitin cewa za a bude musu kofofinsa a ko da yaushe, ya kuma yi alkawarin hada kai don samun ingantacciyar hanyar sarrafa filaye.

Tun da farko, shugaban kwamitin kasa na majalisar kuma mamba mai wakiltar Bunkure, Alhaji Hafizu Gambo Bunkure ya ce sun je ma’aikatar ne domin tabbatar da alakar da ke tsakanin kungiyoyin biyu da kuma taya kwamishinan murnar nadin nasa.
Don haka Hafizu Gambo ya bukaci ma’aikata da sauran ma’aikatan ma’aikatar su yi aiki tukuru tare da ba kwamishinan hadin gwiwa domin ciyar da ma’aikatar gaba.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki