Hajj 2024: Kungiyar Fararen Hula Ta Yi Kira Ga Babban Bankin Najeriya Ya Sauya Tunani Kan Biyan Kudin Guzurin Alhazai

An shawarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya yi watsi da ra’ayin bayar da kudin  (BTA) ta hanyar katin biyan kudi.

Kungiyar fararen hula masu daukar rahotannin aikin Hajji  (IHR) ne suka bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da babban jami'inta na kasa Ibrahim Mohammed ya fitar.

Kungiyar ta ce kasa da sa’o’i 24 da fara jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki, babban Bankin ya umarci wasu bankunan kasuwanci da su biya maniyyatan dala 200 kacal daga cikin dala 500 da ake sa ran kowane mahajjaci zai samu yayin da sauran dala 300. za a bayar a kan katin cirar kudi 

“Alhazai na bana sun riga sun shiga cikin rashin tabbas da yawa tun daga manufofin sayayya da suka haifar da hauhawar farashin Hajji zuwa raguwar kudin guzuri. Wannan shawarar da babban bankin ya yanke zai kara musu bala’i ne kawai”.

“ Sanin kowa ne cewa mafi yawan alhazanmu sun fito ne daga karkara kuma ba su da masaniyar harkar hada-hadar kudi, yawancin ma ba su san yadda ake amfani da katin ATM ba. 

Har ila yau, galibin injinan ATM a Saudiyya ana daidaita su da harshen Larabci wanda ke haifar da kalubale ga ma wadanda suka kware da harkar E-transaction.

"Haka kuma, galibin masu sayar da abinci, ana caje su da yawa saboda amfani da na'urorin ATM a kasashen waje, kuma da karancin BAT da aka riga aka yi, amfani da katunan na janyewa a Saudi Arabiya zai kara wa mahajjata wahala," in ji kungiyar 

Kungiyar ta fararen hula ta kuma bayyana cewa, akwai karancin na’urorin ATM da ake da su a kusa da yankunan Misfalah/Kudai da Shahrah Mansur inda akasarin mahajjatan Najeriya ke zama, wannan rashin samun damar shiga kuma zai zama babbar matsala. 

Kimanin kashi 75 cikin 100 na alhazan Najeriya ne suka fara zuwa karon farko wadanda galibinsu ke samun wahalar gano matsuguninsu a Makkah saboda yawan cunkoson jama’a da gine-ginen na musamman – ta yaya za su iya gano na’urar ATM a irin wannan yanayi?

Sanarwar ta kara da cewa mafi yawan maniyyatan kuma za su fuskanci wahalar biyan kudin hidimar da suke amfani da katin.

“Sayen ruwan sha da sauran kayan masarufi zai zama matsala ga mahajjata a bana, idan babban Bankin Najeriya ya dage sai ya ba su katin cirar kudi na ATM 

Idan ba a manta ba, yana da sauƙi ga talakawa su rike kuɗinsu fiye da kati, saboda haka, yanayin asarar katunan alhazai ya yi yawa sosai. Yakamata a tsara manufofin gwamnati domin saukakawa dan kasa rayuwa ba tare da dagula lamarin ba.

“Saboda haka muna kira ga CBN da ya gaggauta janye hukuncin ya biya maniyyatan kudi, hakan ne zai taimaka musu da kuma rage musu radadin da ke tattare da aikin hajji na shekaru da kuma ba su damar maida hankali wajen gudanar da aikin hajjin cikin kwanciyar hankali. .IHR ta kara da cewa.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki