Kashi 28.5 Na Kanawa Na Fama Da Hawan Jini — Kwamishinan Lafiya



A duk Nijeriya cutar hawan jini ta fi ƙamari a tsakanin al’umma Jihar Kano.


Gwamnatin Kano ta ce, kashi 28.5 cikin 100 na mutanen jihar masu shekaru tsakanin 30 zuwa 79 na fama da cutar hawan jini inda aka gano kusan kashi biyu bisa uku (60.7 cikin 100) sabbin waɗanda suka kamu da cutar.


Kwamishinan Lafiya na jihar, Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a bikin ranar hawan jini ta duniya na shekarar 2024 mai taken: “Ku Auna Hawan Jininku, Ku Daidaita Shi Domin Samun Rayuwa Mai Tsawo”.


Ya ce, “Hawan hawan jini ne babban abin da ke haifar da ɗimbin matsalolin lafiya kamar shanyewar ɓarin jiki, ciwon zuciya da ciwon ƙoda da sauransu.


“Yawancin mutanen da ke fama da hawan jini ba su san cewa suna ɗauke da cutar ba saboda ba a gani wasu alamominta.


“Sau da yawa, mutane sun fi fahimtar cewa suna ɗauke da cutar bayan sun kamu da ciwon zuciya ko shanyewar ɓarin jiki.

“Kimanin manyan mutane biliyan 1.28 masu shekaru 30 zuwa 79 a duniya suna fama da hawan jini.

“Sannan an kiyasta cewa adadin masu hawan jini a duniya zai ƙaru zuwa fiye da kashi 31 cikin 100 na mutanen duniya nan da shekarar 2025.


“A yanzu alƙaluman masu hawan jini a Najeriya ya kai kashi 27.6 cikin 100, inda a Jihar Kano, abin da ya fi ƙamari.

“A Jihar Kano, akasarin masu fama da cututtuka da ke da nasaba da zuciya sun samo asali ne daga hawan jini inda alƙaluman ya kai kashi 28.5 cikin 100 daga ciki, wanda daga ciki kusan kashi biyu bisa uku (kaso 60.7 cikin 100) a baya bayan aka gano suna fama da wannan matsala.”

Ya ƙara da cewa, a wani ɓangare na ayyukan tunawa da Ranar Hawan Jini ta Duniya na shekarar 2024, za a kafa cibiyar yi wa jama’a gwajin cutar hawan jini a Ƙaramar Hukumar Gwale da ke Kanon.
(AMINIYA)


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki