Gwamnan Kano Ya Kaddamar Da Aikin Gadar Sama Mai Musayar Hannu Kan Naira Biliyan 15 A Kano


Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aza harsashin samar da gadar sama musayar hannu kan kudi Naira biliyan 15 a kofar Dan'agundi da ke cikin birnin Kano a wani bangare na hangen nesa na inganta zirga-zirgar ababen hawa a tsohon birnin.

Gwamnan wanda ya ziyarci wurin da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata tare da wasu mambobin majalisar zartarwa, ya tabbatar da ganin gwamnatinsa na ganin an mayar da tsakiyar birnin zuwa matsayin babban birni.

Za a iya tunawa cewa Gwamna Yusuf a watan Disamba, 2023, ya ba kamfanin CCG Nigeria Limited aikin na biliyoyin nairori tare da umarnin kammalawa watanni goma sha takwas. 

An bayar da wannan ayyuka da yawa tare da wata gadar musanyar hannu a shataletalen  Tal'du kuma a cikin tsakiyar gari, don sauÆ™aÆ™a cunkoson ababen hawa.

"Mun kirkiro hanyoyin da za a iya amfani da su kuma ana sa ran masu ababen hawa za su bi ka'idoji don kare lafiya tare da ba da damar gudanar da aikin yadda ya kamata."

Gwamna Abba Kabir ya kuma aza harsashin ginin makamancin wannan aiki a zagayen Tal'udu na naira biliyan 12 wanda aka fara bayar da shi a lokaci guda tare da titin sama da kasa guda uku da na kasa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar, ya ce samar da ababen inganta rayuwa wani bangare ne mai matukar muhimmanci a wannan gwamnati inda gwamna Yusuf ke ware dimbin albarkatu ga fannin ilimi.

Da yake mayar da jawabi bayan kaddamar da harsashin ginin, Manajan dake kula da aiki na kamfanin CGC Nigeria Limited Mr. Gee Wang da kwamishinan ayyuka da gidaje Engr. Marwan Ahmad ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya gabatar inda ya ce za a kammala aikin cikin wa’adin da akakayyade.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki