Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Jihar Bauchi, Ta Jaddada Kudirinta Na Yin Hadin Gwiwa Da Masu Ruwa Da Tsaki Don tunkarar

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi, ta jaddada kudirinta na yin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki wajen tunkarar kalubalen da ake fuskanta a aikin Hajjin shekarar 2024.

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, yace Sakataren zartarwa na Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar mata musulmi ta Najeriya FOMWAN reshen jihar Bauchi a ziyarar ban girma a ofishinsa.

Ya bayyana FOMWAN a matsayin kwararre kuma ya amince da rawar da suke takawa wajen hada hanyoyin sadarwa tsakanin hukumar da alhazai.

Imam Abdurrahman ya jaddada cewa hukumar a shirye take ta ba da hadin kai ga duk wata kungiya ko jama'a da ke son bayar da gudummawar kasonta don samun nasarar aikin Hajji.

A nata jawabin Amirah FOMWAN reshen jihar Bauchi wanda Haj ta wakilta. Aishatu Shehu Awak wadda ta zama shugabar kungiyar FOMWAN kuma shugabar kwamitin daawa ta jihar Bauchi, ta ce sun je  hukumar ne domin yin rijistar ci gaba da tallafa wa hukumar ta fannin ilmantar da alhazai da fadakarwa.
Ta yi amfani da damarta wajen jinjina wa Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad kan yadda ya tallafa wa alhazai da kashi 50% na karin kudin aikin Hajjin da Hukumar NAHCON ta sanar.

A wani labarin kuma, Sakataren zartarwa na Hukumar Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ya gargadi Ma’aikatansa da su guji sauke nauyin da aka dora musu.
Ya yi wannan gargadin ne a wata tattaunawa da ma’aikatan sa a yau a dakin taro na hukumar.

Imam Abdurrahman ya ja hankalin ma’aikatan da su tashi tsaye, ya kara da cewa ba zai lamunci sakaci a wajen aiki ba.

Daga nan ya yabawa ma’aikatan bangaren fasahar sadarwa bisa kwazon da suka nuna wanda ya kai ga samun bizar kashi 90% na maniyyatan Jahar a halin yanzu.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki