Majalisar Dokokin Kano Za Ta Yi Wa Dokar Masarautu Gyara
A shekarar 2019 dai aka yi wa dokar masarautu a jihar gyara inda aka ƙirƙiro ƙarin masarautu gudu huɗu masu daraja ta ɗaya a jihar.
Majalisar ta amince da hakan ne a zaman da ta yi na ranar Talata.
Majalisar Dokokin Kano ta amince a dawo da dokar masarautu ta jihar domin yi mata kwaskwarima.
Majalisar ta amince da hakan ne a zaman da ta yi a ranar Talata.
A shekarar 2019 gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa dokar masarautu ta jihar gyara inda aka ƙirƙiro ƙarin masarautu gudu huɗu masu daraja ta ɗaya.
Masarautun sun haɗa da Gaya da Ƙaraye da Rano waɗanda aka ɗaga darajarsu zuwa masu daraja da ta ɗaya daidai da masarautar Kano.
Sai kuma Masarautar Bichi da aka ƙirƙiro, abin da ya sa Kano ta zama tana da masarautu biyar masu daraja ta ɗaya.
Masu adawa da matakin a lokacin sun soki ƙirƙiro sababbin masarautu a Kano domin a cewarsu hakan zai rusa tarihin masaratuar Kano na daruruwan shekaru, inda masarautar take da ƙima a idon duniya saboda faɗinta da kuma tasirinta.
Amma mutanen yankunan da aka ƙirƙiro wa masarautun sun yi maraba da matakin, suna cewa hakan zai ƙara kawo musu ci gaba da bunƙasa.
(TRT Hausa)