Jami’an NAHCON Dake Makkah Sun Shirya Karbar Alhazan Da Suka Gama Zamansu Na Madinah
A yayin da hakan ya tabbata ne saboda yadda Jami’an suka hada karfi da karfe tsakanin maaikatan NAHCON dake Makkah da wadanda ke Madinah wajen seta duk bukatun da Alhazan ke da Su a Makkah da suka shafi masaukai da wajajen dafa abinci.
A zagayen rangadin da Jami’an suka kai wajen dafa girkin da masaukan Alhazan da anjumar yau dinnan ne za su fara baro Madinah don shigowa Makkah bayan kammala kwanakinsu hudu a Madinah din, kampanonin dake dafa abinci sun tabbatarwa NAHCON za su ciyar da Alhazan ba tare da kwange ba hakazalika masu bada masaukai.
Hakan kuma yasa NAHCON ta sake jaddada lallai idan ba a bai Alhazanta abunda yarjejeniyar da suka rattabawa hannu ba to kampanonin su kwana da sanin za a ma iya soke kwangilar take-yanke.
Zuwa wani lokaci Kadan yau din ne za a tabbatar da sa idon Jami’an NAHCON zai sa kampanonin bada hidimomi su zage damtse don kada kilu ta jawo bau. Haka kuma yadda Alhazan bana suka dandana dadin Madinah na tsawon kwanaki hudu, haka za su fahimci yanzu dai duk kanwar jaa ce sanda suka iso Makkah ma.
(NAHCON MEDIA)