Hajj2024: Anyi Kira Ga Kason Farko Na Maniyyatan Bauchi Su Kasance Jakadun Jahar Nagari
Amirul Hajj 2024 ma jahar Bauchi, ya bukaci alhazan jihar da su kasance jakadu nagari tare da nuna biyayya da mutunta ka’idojin da Saudiyya ta shimfida.
A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, yace Amirul hajj wanda kuma ya kasance Mai Martaba Sarkin Dass Alh. Usman Bilyaminu Othman ya yi wannan nasihar ne a wajen bankwana na musamman ga rukunin farko na maniyyata da aka gudanar a filin jirgin saman Sir Abubakar Tafawa Balew
Sarkin Dass ya bayyana cewa jajircewar da gwamnatin Gwamna Bala Abdulkadir ta yi kan al’amuran addini alama ce da ke nuna sha’awar sa ga rayuwar al’umma.
A lokacin da yake yi musu fatan yin Hajji karbabbiya, Amirul hajj din ya bukaci maniyyatan da ke da damar zuwa aikin hajjin bana da su yi wa Gwamna addu’a. Jihar Bauchi da kasa baki daya.
A nasa jawabin shugaban kwamitin yada labarai na tawagar Amerul hajji Alh. Yayanuwa Zainabari ya bayyana yadda aikin ya gudana cikin sauki, inda ya danganta nasarar da Gwamnan ya samu, don haka ya jaddada kudirin gwamnati na tabbatar da jin dadin alhazai a duk lokacin da ake gudanar da atisayen.
Tunda Farko a nasa jawabin ga manema labarai gabanin tashin jirgin farko, Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ya bayyana cewa jirgin farko na Bauchi ya yi nasarar tashi daga filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi zuwa Saudiyya. tare da alhazai 530.
Imam Abdurrahman ya kara da cewa hukumar Alhazai ta Bauchi ta shirya fara tantance jirgin na biyu daga gobe Asabar 18 ga watan Mayu 2024 da karfe 10:00 na safe.
Ya yaba da bin ka’idojin da aka samu daga rukunin farko na maniyyatan, ya kuma bukaci rukunin da suyi koyi dasu