Hajjin 2024: Sakataren Hukumar Alhazai Na Bauchi Bayyana Muhimmancin Yi Wa Maniyyata Rigakafi


Sakataren Zartarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ya bayyana jin dadinsa da tsare-tsaren Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta jiha na fara gudanar da allurar rigakafin cututtukan da za a iya kauce musu kamar su diphtheria, polio da kyanda.

 A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, yace Imam Abdurrahman ya bayyana jin dadinsa a lokacin da ya ziyarci wajen ajiye magunguna na jihar da ke asibitin kwararru na Bauchi, a fadar jiha.

 Ya bayyana cewa ya je gurin ajiyar ne domin ganewa idonsa shirye-shiryen hukumar lafiya matakin farko na jihar gabanin gudanar da allurar rigakafin cutar a fadin jihar.

Babban sakataren wanda ya nuna farin cikinsa kan abin da ya gani a gurin ajiye magungunan, ya yi nadamar sanar da rashin fara aikin rigakafin a yau kamar yadda aka tsara tun da farko, a cewarsa, sakamakon cikas da aka samu ne wajen kawo maganin a jiha.
 
 Ya bayyana wasu ’yan sauye-sauye a tsarin gudanarda rigakafin, inda ya ce maniyata daga karamar hukumar Bauchi da shirin adashen gata wato HSS, na hukumar alhazai da Alhazan da gwamnati ta dauki nauyin su, za'a mu rigakafinsu a gobe Asabar, *11 zuwa Litinin 13 ga Mayu, 2024* daga *10; 00 na safe zuwa 4;00* na yamma a asibitin kwararru na Bauchi (BACAS).

 Imam Abdurrahman ya kara da cewa, za a raba alluran rigakafin a dukkanin manyan asibitocin kananan hukumomi a jiha, ta yadda Alhazan kananan hukumomi za su samu saukin halartar cibiyoyi daban-daban kamar yadda aka tsara daga *Lahadi 12 ga Mayu, 2024.*

 Yayin da yake nanata cewa rigakafin ya yi daidai da sharuddan da hukumomin lafiya na kasar Saudiyya suka gindaya na maniyyata a lokacin aikin Hajji, Imam Abdurrahman ya bukaci maniyyatan da su tabbatar da sunyi allurar, Kuma zasu taho da slip din fom din aikin hajjin su don tantance su kafin musu rigakafin.

 A wani labarin kuma, Bankin Jaiz Bank reshen jihar Bauchi ya gabatar da wani tallafi ga babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta Bauchi.

 Da yake gabatar da tallafin, a madadin bankin, Manajan reshen Bankin dake Bauchi Muhammad Muhammad Gidado ya yi alkawarin cigaba da samun kyakyawar hadin gwuiwa da hukumar alhazai domin tallafawa don jin dadin alhazai.

 Ya kuma jaddada cewa Bankin ya samar da kyawawan matakai don tabbatar da walwalan maniyyata.

 A lokacin da yake karbar tallafin a madadin alhazai, Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ya yaba da wannan karimcin, inda ya ce dukkan alhazan HSS sun amfana da wannan shirin Bankin.

 Ya ce "Na gamsu matuka da jajircewar da kuka yi na kyautata jin dadin alhazanmu ta hanyar ba su kyauta da zai taimaka musu wajen gudanar da aikin hajjin su."

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki