Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sake Yin Wasu Karin Nade-Nade A Gwamnatinsa
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin wasu mutane a matsayin masu bashi shawara na musamman a bangarori daban-daban
A sanarwar da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce wadanda aka nada din sun hada da :
1. Kanal Abubakar Usman Garin Malam mai ritaya a matsayin mai bawa Gwamna shawara na musamman Kan kula da harkokin iftila'i.
2. Malam Usamatu Salga, mai bada shawara na musamman Kan al'amuran addini
3. Abduljabbar Muhammad Umar , mai bawa Gwamna shawara Kan harkokin zuba Jari da Kuma kulla alaka da bangarorin da ba na gwamnati
4. Aminu Abba Ibrahim, mai bawa Gwamna shawara kan albarkatun kasa
5. Injiniya Nura Hussain, mai bawa Gwamna shawara kan harkokin ciniki
6. Jamilu Abbas, mai bawa Gwamna shawara na musamman Kan kungiyoyin tsumi da tanadi
7. Muhammad Jamu Yusuf, mai bawa Gwamna shawara na musamman kan dangantaka da Kasashen Waje da na waje
8. Balarabe Ibrahim Gaya, mai bawa Gwamna shawara na musamman Kan shirye-shiryen bayar da Tallafin na musamman
9. Isyaku Ali Danja, mai bawa Gwamna shawara Kan harkokin majalisa
10. Comrade Baffa Sani Gaya, mai bawa Gwamna shawara na musamman Kan harkokin kwadago
11. Injiniya Abdullahi Shehu, mai bawa Gwamna shawara na musamman kan tsaftar muhalli
12. Umar Musa Gama, mai bawa Gwamna shawara na musamman Kan shirin ciyar da abinci na 'yan makaranta
13. Habibu Hassan Elyakub, mai bawa Gwamna shawara na musamman kan ci gaban harkokin koyar da sana'o'i
14. Jamilu Abubakar Dambatta, mai bawa Gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai
15. Umar Uba Akawu, mai bawa Gwamna shawara na musamman a ofishin gwamnatin Kano na Abuja
Sanarwar ta ce Dukkanin nadin sun fara aiki ne nan take.