Za A Kashe N61m Wajen Binne Mutum 103 Da Aka Kashe A Zanga-Zangar #EndSARS A Legas
Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce bayan Gwamnatin Jihar Legas ta amince ta kashe Naira miliyan 61.2 domin binne mutum 103 da aka kashe yayin zanga-zangar #EndSARS a Jihar shekara uku da suka wuce.
A baya dai, gwamnatin Jihar da ma sojoji sun sha karyata rahoton kwamitin jin bahasin da aka kafa kan zanga-zangar, wanda ya ce jami’an tsaro sun bude wuta a kan masu zanga-zangar a Lekki Toll Gate ranar 20 ga watan Oktoban 2020.
An dai gudanar da zanga-zangar ce karshen shekara ta 2020, inda wadanda suka yi ta suka nemi a rushe sashen nan na Rundunar ’Yan Sanda mai yaki da ’yan fashi (SARS), saboda kaurin sunan da ya yi wajen zargin take hakkin dan Adam.
Zanga-zangar dai, wacce a lokacin aka shafe tsawon makonni ana yin ta, da farko ta lumana ce, amma daga bisani ta rikide ta koma ta fasawa tare da sace kayayyaki a rumbunan gwamnati da na jama’a, kona ofisoshin ’yan sanda da kuma lalata dukiyoyi masu yawa.
Wasikar dai ta jawo ce-ce-ku-ce matuka, inda wasu masu fafutuka suke cewa hakan tamkar amincewa ne daga gwamnatin kan kisan mutanen, wanda a baya ta sha karyata cewa an kashe su.
To sai dai a wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Legas, Dokta Olusegun Ogboye, ya fitar da daren Lahadi, ya yi ikirarin cewa babu ko daya daga cikin gawarwaki 103 da aka kashe a Lekki Toll Gate.
Ya ce, “An tsinto su ne a unguwanni daban-daban sakamakon fada da aka yi a yankunan Fagba, Ketu, Ikorodu, Orile, Ajegunle, Abule-Egba, Ikeja, Ojota, Ekoro, Ogba, Isolo da Ajah na Jihar Legas.