Hajj 2023: Gwamna Yusuf ya ba da gudummawar naira miliyan sittin da biyar ga maniyyatan 6,166

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayar da gudummawar Naira miliyan 65 ga maniyyata Jihar Kano 6,166, wadanda suka yi aikin Hajjin shekarar 2023 a kasa mai tsarki a matsayin ‘Kyautar Sallah’.


A cikin sanarwar da babban sakataren Yada labaran gwaman, Sunusi Bature Dawakin Tofa, tace da Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu Danbappa ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wajen taron bayan Arafat da ya yi da jami’an alhazai a Makka.


Ya ce kowane mahajjaci za a ba shi Riyal Hamsin

Daraktan ya ce an yi hakan ne domin nuna yabawa da kyawawan halayen da mahajjatan suka nuna a kasa mai tsarki.

Ya bukaci alhazan da su kashe kyautar gwamna da na guzirimsu ta hanyar da ta dace  su kuma guji kashe kudaden da za su iya hana su komawa kasar bayan sun kammala ankinsu na ibada 

Daga nan ya bukaci alhazan da su ci gaba da kokarin nuna kyakykyawan kimar jiha da kasa a kasa mai tsarki.

Ya ce, “Alhazan za su dawo daki-daki kamar yadda suka zo kasa mai tsarki

Danbappa ya ci gaba da bayanin cewa hukumar za ta fara bayar da babbar jaka ga maniyyatan jihar Kano tare da kyautar Sallah da gwamna ya bayar.

Babban Daraktan ya bukaci alhazan da su kasance masu hakuri da kuma yi wa Najeriya da jihar Kano addu’a ta musamman domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Danbappa ya kuma yi addu’ar Allah ya karbi aikin Hajjin su ya kuma dawo da su gida lafiya.



Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki