Hajj 2023: Kashi Na Farko Na Alhazan Kano Sun Bar Makkah Zuwa Jiddah Domin Dawowa Najeriya

A ranar Asabar da ta gabata ne rukunin farko na alhazan Kano da suka yi aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya, suka tashi daga Makka zuwa Najeriya.

A sanarwar da da Jagoran tawagar 'yan jaridu na aikin Hajji na Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, ta ce alhazan sun tashi daga Makka zuwa filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz, Jeddah, da misalin karfe goma na safe agogon Saudiyya.

Ana sa ran jirgin nasu zai tashi da yamma a wannan rana.

Tun a daren Juma’a ne dai aka fara gudanar da tafiyarsu tare da tantance jakunansu na hannu domin tabbatar da aiki da tsarin hukumar alhazai ta kasa.

A safiyar ranar Asabar alhazan tare da jakunkunansu sun taru domin shiga manyan motocin bas na alfarma zuwa filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz na Jeddah.

Wasu daga cikin mahajjatan da aka zanta da su, Zubairu Hudu Sani daga Doguwa, Sirajo Hudu daga Tudunwada, Maryam Abdullahi Garun Malam da Hadiza Hamisu daga kananan hukumomin Bebeji sun gode wa Allah da ya ba su damar yin aikin hajjin bana tare da yaba wa Gwamna Yusuf kan aikin hajjin na bana.

A wata hira da manema labarai jim kadan bayan kammala bankwana da mahajjatan, daraktan ayyuka na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Alhaji Kabiru Muhammad Panda ya bayyana godiyarsa ga Allah madaukakin sarki bisa nasarar gudanar da ayyukan.

Alhaji Panda ya ce ana sa ran kowane mahajjaci zai shafe kwanaki 40 zuwa 43 a kasa mai tsarki kafin a dawo da shi Najeriya ta jirgin sama.

A cewarsa tafiyar komawa gida za ta kasance ne kawai a kan tsarin farko na tafiyar mahajjata zuwa kasa mai tsarki, 'farko da izinin farko' don yin adalci wajen sauke aikin.


"Al'adar wanda ya zo farko shi zai koma a farko, za a kiyaye dawowar farko a matsayin ka'ida kuma daidai da ka'idojin Saudiyya na adalci da daidaito," in ji shi.

A yayin da yake kira ga maniyyata da masu aikin hajji da su gudanar da tafiye-tafiyen zuwa gida cikin tsari, amma ya bayyana cewa hukumar jin dadin alhazai ta jiha karkashin ingantacciyar jagorancin Alhaji Laminu Rabiu tana aiki ba dare ba rana domin ganin an samu nasarar aikin hajjin.

Daraktan ya nuna godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da yake bayarwa wajen samun nasarar aikin Hajjin bana.


A ranar Litinin 17 ga watan Yuli ne ake sa ran kashi na biyu da na uku na alhazan Kano za su bar Makka.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Litinin 5 ga watan Yuni, 2023 ne aka fara jigilar Alhazan bana daga Kano zuwa Saudiyya.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki