Shirin Karo Karatu A Kasashen Waje: Kason Farko Na Daliban Kano Zasu Tafi Nan Da Watan Satumba- Gwamna Abba K Yusuf

A yayin da ake kokarin ganin an aiwatar da manufar gwamnatin jihar Kano ta shirin bayar da tallafin karatu na digiri na farko a kasashen waje, ana sa ran kashi na farko na daliban da za su ci gajiyar shirin za su bar kasar nan da watan Satumba na wannan shekara.

Gwamnan jihar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a fadar gwamnati a ranar Asabar a lokacin da ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Bichi Alh Nasiru Ado Bayero da ‘yan majalisar Masarautar da suka kai gaisuwar Sallah ga Gwamnan.

Alh Abba Kabir Yusuf ya kara jaddada kudirin gwamnatin sa bisa fifikon da ake bukata a bangaren ilimi domin gwamnati na shirin sake bude cibiyoyi 20 da gwamnatin da ta shude ta rufe, da makarantun Islamiyya da kwalejojin fasaha a lungu da sako na jihar. jihar da ra'ayin samar da ingantaccen ilimi ga matasa a jihar.

Gwamnan ya godewa Sarkin yayin da ya yaba da rawar da sarakunan gargajiya ke takawa a matsayin masu kula da al’adu da yada zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba.

Mai Martaba Sarkin Kano Alh Nasiru Ado Bayero ya ce ya ziyarci gidan gwamnati ne domin yi wa gwamna barka da Sallah tare da yin amfani da wannan damar wajen yin kira da a samar wa manoma taki a farashi mai rahusa, da bukatar yakin noman itatuwa da hako rijiyoyin burtsatse. .

Alh Nasiru Ado Bayero ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gayyato masu zuba jari don bunkasa tattalin arzikin jihar tare da godewa gwamnan bisa nada dan masarautar Dr Abdullahi Baffa Bichi a matsayin sakataren gwamnatin jihar Kano.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki