Gwamnatin Kano Ta Bada Tallafin Riyal 30,000 Ga Alhazai 50 Da Suka Rasa Kudin guzirinsu

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da tallafin Riyal 30,000 na kasar Saudiyya ga Alhazanta 50 da suka yi asarar Kudin guzurinsu a kasar Saudiyya.

A sanarwar da mai rikon mukamin shugaban tawagar yan jaridu dake kawo rahoton Aikin hajjin bana, Nasiru Yusuf Ibrahim, ya ce Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jiha, Alhaji Laminu Rabiu Danbappa ne ya sanar da hakan a ranar Talata a wata ganawa da manema labarai a birnin Makkah.

Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bayyana cewa, bisa ga girmansa ya bayar da amincewar fitar da kudaden a cikin kasafin kudin da hukumar ta yi da nufin tallafa wa wadanda abin ya shafa amma ba don a biya su diyya ba da fatan abin da ya faru zai zama kaffara.

Ya kara da cewa wadanda suka ci gajiyar tallafin sun karbi rabin kudaden daga Riyal na Saudiyya 750 zuwa Dalar Amurka 500.

A cewarsa babbar wadda ta ci gajiyar tallafin ita ce wata mace daga karamar hukumar Gwale wadda ta yi asarar dalar Amurka 1,000 sannan ta karbi dalar Amurka 500.

Da yake zantawa da manema labarai daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar Yunusa Ibrahim daga karamar hukumar Rimingado, wanda ya rasa jakarsa ta kugu da dala 500 da kudin gida N100,000 a hanyarsa ta fita daga harami bayan da aka yi masa dawafi, ya ce an ba shi Riyal 750 na Saudiyya ne bisa ga jin dadin Gwamnan.

Ana sa ran kammala jigilar Alhazan Kano a ranar Lahadi

Da yake karin haske dangane da batun jigilar mahajjatan da zasu dawo gida, Darakta Janar na kayyakin, ya ce kawo yanzu an yi jigilar sama da mutane 3,000 a cikin jirage shida, ya kara da cewa rukunin na bakwai da na takwas za su tashi ne nan da tsakiyar makon nan.

Ya ci gaba da cewa, hukumar alhazai ta Najeriya ta ba su tabbacin kaucewa duk wata matsala don dawo da alhazan , kafin ranar Lahadi 31 ga wannan wata.



Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki