Farfesa Abdurrashid Garba Ya Zama Shugaban Jami'ar Isyaka Rabiu Ta Kano

Jami'ar Khalifa Isyaku Rabiu  Kano (KHAIRUN) ta sanar da nadin Farfesa Abdulrashid Garba a matsayin shugaban jami’ar na farko. 

A sanarwar da sakataren gudanarwa na Jami'ar Malam Yusuf Datti ya sanyawa hannu, ta ce, tare da aikin da ya shafe sama da shekaru 33 na koyarwa, bincike da ƙwarewar aiki na al'umma, Kwamitin Amintattu na Jami’ar a karkashin jagorancin Emeritus Farfesa Muhammad Sani Zahradeen ne ya amince da nadin.

A baya ya taba zama mataimakin shugaban jami’ar Bayero ta Kano, da babban jami’in hukumar shirya jarabawar ta kasa NECO da kuma mai baiwa ministan ilimi shawara na musamman wanda hakan ke kara bayyana kudirinsa na bunkasa ilimi.

Jami'ar ta bayyana gamsuwarta ga ikon Farfesa Abdulrashid Garba na jagoranci da kuma jagorantar hanyarta zuwa ga kyakkyawar makoma da ban mamaki.

An haifi Farfesa Garba a ranar 11 ga Afrilu, 1959 kuma yana da aure da ’ya’ya tara.

Da fatan za a kasance tare da mu domin taya Farfesa Abdulrashid Garba murnar nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin shugaban jami'ar Khairun.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki