Yanzu-Yanzu : Dan Takarar Gwamnan Kano Na Jam'iyyar LP, Bashir I Bashir Ya Koma APC

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour Party, LP, a jihar Kano, Bashir Bashir, ya fice daga jam’iyyarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

A ranar 21 ga watan Janairu, dan takarar gwamnan ya kaurace wa taron gangamin jam’iyyar a Kano tare da shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Mohammed Zarewa; kodinetan yakin neman zaben Peter Obi na jiha, Balarabe Wakili da; dan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Idris Dambazau.

Wata majiya da ke kusa da dan takarar ta tabbatar da sauya shekar Mista Bashir da wasu jiga-jigan jam’iyyar LP zuwa APC a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta ce babban dalilin da ya sa suka sauya sheka shi ne na ware manyan masu ruwa da tsaki a Arewa wajen yanke shawara da kuma rashin samun cikakkiyar alkibla kan maslahar Arewacin Najeriya. .

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki