INEC Ta Gargadi Masu Sanya Idanu Kan Zaben Najeriya

Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC, ta gargaɗi masu aikin sa ido kan yadda zaɓukan ƙasar za su gudana su kiyaye da dokoki da ƙa'idojin ƙasar sannan su guji katsa-landan a abin da ba su da hurumi a kai.

INEC ta yi gargaɗin ne a lokacin da ta gudanar da taron ƙarin haske game da dokokin aikin sa idon da bayar da bayanai ga masu aikin na cikin gida da kuma na waje a Abuja, ranar Talatar nan.

Tuni dubban masu sa idon suka hallara a ƙasar domin duba yadda zaɓukan - da za a fara ranar Asabar 25 ga watan nan na Fabarairu - za su gudana, inda za a fara da na shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokoki na tarayya.

Sai kuma ranar 11 ga watan Maris inda za a yi zaɓukan gwamnoni da 'yan majalisun dokoki na jihohi

Dubban masu sanya idanu daga ƙungoyoyi daban-daban na ciki da wajen Najeriya ne suka saurari bayanai daga manyan jami'ai na hukumar zaɓen da suka haɗa da shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu da sauran muƙarraban hukumar game da yadda kowa zai taka rawar da ta dace ba tare da wuce gona da iri ba a kan zaɓukan.

Farfesa Sani Adam wanda kwamishina ne a hukumar zaɓen ta Najeriya ya yi wa BBC ƙarin bayani a kan gargaɗin da suka yi wa masu aikin sa idon, inda ya ce suna so jami'an su kasance mutane masu adalci ba kuma 'yan leƙen asiri ƙasa ba.

Farfesan ya ce suna son su kasance sun dubi abin da ake yi kuma su tabbatar duk ƙa'idojin da aka gindaya musu sun kiyaye da su, sannan a bi zaɓen kamar yadda ake ba tare da an samu tashin hankali ba

Kwamishinan ya ce suna so masu sa idon, su kasance sun bayar da bayani kan abubuwan da suka gani na gaskiya sannan su kasance masu bin dokokin Najeriya da kuma zaɓen.

Bayan wannan kuma kar su yi katsa-landan a ciki, kar su shiga harkar da ba ta shafe su ba.

Jami'in ya ce, ''masu aikin suna da damar bayar da bayanin duk abin da suka gani su tabbatar haka ne.''

Ya ce, ''akwai dokoki waɗanda suka ba masu aikin sa idon, '' mun ƙarfafa gaya masu cewa Najeriya ƙasa ce mai zaman kanta ba ƙasa ba ce da za su zo su yi mata katsa-landan,'' in ji shi.

''Amma su yi aikinsu yadda ake so kuma su yi aiki ne don su taimaka mana wajen ƙara gyara yadda ake zaɓe a Najeriya,'' a cewarsa.

Shi kuwa Salisu Musa mai sa ido daga ƙungiyar 'Country International Human Right Movement', ya gaya wa BBC cewa a matsayinsu na masu sa ido na waje ''dole mu ɗauki ƙa'idojin da suka bayar.

''Amma akwai abubuwan da INEC suka faɗa kusan za mu saurare su mu ji'', in shi ji.

''Amma za mu saka ido duk abin da muka ga ya yi ba daidai ba za mu sa shi a cikin rahoto don kowa ya same shi,'' in ji shi.

Musa ya ce, ''ka san daman kusan ita wannan observers kamar ba ta shiri da INEC saboda abin da ake gani sun zo don su bi ƙwaƙwaf kan me ke faruwa,''

''Ka san ba za ka so ya zamanto ya yi maka babakere a gida ba,'' in ji mai sa idon.

''Ita maganar wannan katsa-landan suna nufin dole mu bi a hankali tun da dukkanmu ƙungiyar da ta zo wajen aikin nan dole muna da tsare-tsarenmu, kuma za mu tabbatar namu bai ƙetare na hukumar zaɓen ba,'' in ji shi.

Shugaban hukumar zaɓen ta Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce wannan zaɓe shi ne wanda ya fi samun masu sa ido na ciki da na waje a tarihin zaɓen Najeriya.
BBC 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki