Atiku Abubakar Zai Kaddamar Da Makarantar Haddar Alkur'ani A Kano


 Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai kaddamar da makarantar sakandaren kwana ta haddar Al-Kur’ani mai dalibai 500 a Jihar Kano.

Atiku zai bude wannan makarantar haddar Al-Kur’ani ce a unguwar Gunduwawa da ke Karamar Hukumar Gezawa, a yayin ziyarar yakin neman zabensa a Jihar Kano, wadda za a gudanar ranar 9 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Wannan makarantar haddar Al-Kur’ani “Na da wurin kwanan dalibai mata 250, maza 250, kuma za su rika haddace Al-Kur’ani a cikin wata bakwai, kafin su tafi makarnatun gaba da sakandare,” inji kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku a Jihar Kano, Sule Ya’u Sule.

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ne dai ya gina makarantar ta haddar Al-Kur’ani mai daukar dalibai 500 a matsayin aikinsa na raya alu’m

Sule Ya’u Sule ya sanara ranar Laraba cewa, Atiku zai kaddamar da makarantar ce a ranar taron yakin neman zabensa, ko kuma washegari.

A cewarsa, “Wazirin Adamawa zai zo Kano ranar 9 ga Fabrairu, don haka jama’ar Kano ku shirya ganin dan takara mai karsashi da koshin lafiya.

“Atiku ba ba irin ’yan takarar na ba newadanda cikinsu wani da kyar yake magana,  wani ko makirfon ba ya iya rikewa, wani kuma cewa ya yi ya zo Kano ne don ya yi rawa.”

(AMINIYA)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki