Buhari ya gana da Emefiele da EFCC kan karancin Naira

 


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri  da Gwamnan Babban Bankin Kasar, CBN, Godwin Emefiele da shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa , EFCC, AbdulRasheed Bawa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari  game da halin da kasar ke cikin na karancin takardar kudin Naira

Kazalika gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da takwaransa na Kebbi, Atiku Bagudu, su ma sun halarci zaman na yau Talata.

An gudanar da wannan zaman ne a daidai lokacin da  ake fama fa matsanancin karancin takardar kudin Naira wanda ya haddasa zanga-zanga a wasu sassan Najeriya tare da kaddamar da hari kan wasu bankuna da jami’an tsaro.

A Juma’ar da ta gabata  ne, shugaba Buhari ya roki ‘yan kasarr da su ba shi wa’adin kwanaki bakwai domin magance matsalar karancin takadar Nairar wadda ta samo asali sakamakon shirin Babban Bankin CBN na sauya fasalin Naira 1000 da 500 da kuma 200.

Nan da ranar 10 ga wannan wata ne, wa’adin da shugaban ya nema zai cika, yayin da ‘yan kasar suka zura idanu domin ganin yadda za ta kaya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa nan da ‘yan kwanaki kalilan, yayin da batun karancin Nairar ya yamutsa hazon siyasar kasar, inda har dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ke zargin cewa, zagon-kasa ake yi masa, shi ya sa aka bullo da shirin sauya Nairar gami da kirkirar matsalar karancin man fetur a cewarsa.

 (RFI)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki