Kotun Ƙolin Ta Dakatar Da Gwamnatin Najeriya Dga Aiwatar Da Wa'adin Amfani Da Tsofaffin Kudi

Kotun Ƙolin Najeriya ta dakatar da gwamnatin tarayya daga aiwatar da wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin kasar.

A baya dai CBN ya saka 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin takardun naira 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sauya wa fasali.

Jihohin arewacin ƙasar uku, waɗanda suka haɗa da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da ƙarar a gaban Kotun Ƙolin ƙasar suna buƙatar kotun da ta hana Babban Bankin ƙasar aiwatar da wa'adin.

A hukuncin wucin-gadin da suka yanke, alƙalan kotun bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari'a John Okoro, sun dakatar da gwamnatin tarayya da Babban bankin ƙasar da sauran bankunan kasuwanci na ƙasar daga aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar.

Kotun ta kuma ce dole ne gwamnatin tarayya da CBN da kuma sauran bankunan ƙasar su jingine batun aiwatar da wa'adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin a ranar 15 ga watan Fabrairu.

Wannan hukunci na nufin a halin yanzu al'ummar Najeriya za su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin ƙasar har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukuncin ƙarshe.

Batun wa'adin amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar dai ya zama wani batu da ya ɗauki hankula a 'yan kwanakin nan.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki