Kofa ya shirya taron addu'a na musammam ga Tinubu, Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf
Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru da Bebeji, Kano, a yau ya tara malamai 1,000 a garinsa na Kofa a Bebeji, Kano, domin addu’a ta musamman ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da kasar baki daya, Jagoran jam’iyyar NNPP da Ɗarikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, PhD, FNSE da kuma neman nasara ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a Kotun Ƙoli, da kuma addu’ar neman taimakon Allah ga ɗan majalisar.
A sanarwar da hadimin dan majalisar kan harkokin yada yada labarai, Sani Ibrahim Paki ya sanyawa hannu, yace yayin taron, malaman sun sauke Alƙur’ani sau 1,101, sannan suka yi addu’o’i na musamman.
A taƙaitaccen jawabin da ya gabatar a wajen taron, Hon. Jibrin ya ce alaƙarsa da Shugaba Tinubu ba ɓoyayya ba ce. Ya kuma ce Kwankwaso ne maigidanshi, sannan zai ci gaba da iya ƙoƙarinsa wajen ganin an samu kyakkyawar alaƙa a tsakanin Tinubun da Kwankwaso.
Jibrin ya kuma ce NNPP jam’iyya ce mai farin jini kuma har yanzu kofarta a buɗe take domin yin aiki tare, ƙawance da kuma haɗaka da APC, har ma da PDP da LP, da ma duk jam’iyyar da ta nuna sha’awar yin hakan, matukar za ta yi haka ne don amfanin ’yan Najeriya.
Ɗan majalisar mai hawa hudu ya kuma yi alkawarin yin amfani da gogewarsa da sanin mutane wajen tattaunawa da masu faɗa-a-ji a siyasar Kano, domin ganin an magance duk wata matsala da za ta iya magantuwa sannan a kawar da duk wata fargaba da ake da ita a jihar a yanzu kan shari’ar kujerar Gwamnan Jihar.
Kazalika, bayan kammala taron addu’ar, kamar yadda ya saba, Hon. Jibrin ya kuma karɓi baƙuncin ɗaliban firamare 5,000 daga faɗin mazaɓarsa, inda ya raba musu kayayyakin karatu sannan ya yi musu albishir ɗin nagartattun shirye-shirye da gwamnatin jiha da ta tarayya suke yi musu don bunƙasa ilimi, musamman a fannin samar da ilimi kyauta da kuma shirin ciyar da ’yan makaranta.