Shugaban NAHCON Ya Ziyarci Ofishin Jakadancin Saudiyya na Abuja.
Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya wato NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya kai ziyarar ban-girma zuwa ofishin Huldar Jakadanci na Saudiyya inda ya gana da Jakadan Saudiyya dake Abuja, Ambasada Faisal Ibrahim Al-Ghamidy, a ranar Laraba
A sanarwar da Hukumar ta fitar ta ce, Shugaban ya kai ziyarar ce da nufin bunkasa dangantaka da habakar da hadin-gwiwa tsakanin bangarorin biyu.
Malam Arabi ya jaddada jin dadinsa ganin yadda Jakadan Kasar Saudiyya Ambassada Faisal ke bada cikakken goyon-baya ga Hukumar da tareraya irinta Huldar Jakadanci karkashin Ofishin Jakadancin Saudiyyar.
Sanarwar tace ziyarar, ta bayyana karara yadda dadaddiyar alaqa ta jituwa ke tsakanin NAHCON da Ofishin Jakadancin Saudiyyar, abinda ke nuni da fahimtar-juna da hadin kai dake wanzuwa a tsakanin Kasashen biyu.
A Yayin ganawar, bangarorin biyu
sun zanta batutuwa masu ma’anar gaske, abunda ke tabbatar da muhimmancin tarayyarsu wajen kara inganta gudanar da Al-amurran Aikin Hajji A Najeriya
Shugaban NAHCON ya bayyana jinjinarsa ga cigaba da habakar da temakekeniyar da Ofishin Jakadancin Saudiyya ke baiwa Hukumar Hajjin, abunda ke haifar da samun nasarar gudanar da Aikin Hajji cikin walwala da dadin-rai ga Alhazan Najeriya.
Bisa wannan ci gaba, bangarorin guda biyu sun sha alwashin kara jajircewa da yin tsayin-daka wajen ganin sun kara zama tsintsiya madaurinki daya wajen aiwatar da hadahadar Aikin Hajjin tare da cikakken hadin-gwiwa da zai cigaba da samar da sakamako melai dorewa da wanzar da ingantaccen Hajji ga Alhazai da sauran masu ruwa da tsaki a Harkar Gudanar da Hajji.
Wannan hadin gwiwa dake tsakanin NAHCON da Ofishin Huldar Jakadancin Saudi Arabiya, zai ci gaba da share fagen ingantuwar kai kawo da musayar bayanai da samar da walwala ga dubban Alhazai Maniyyata zuwa Ibadar Hajji.
Hakazalika, Sun daura azama da aniyar gaggauta hanyoyin samarwa Maniyyata jin dadi yadda ya kamata.
A wani ci gaba kuma, nan ba da jimawa ba ne, Hukumar NAHCON zata kammala bincike-binciken korafe-korafen da kamfanonin jirgin yawo suka gabatar a gabanta don tabbatar da ganin wadanda aka tantance ba suda wata matsala domin su gudanar da kai Alhazan shekarar bana ta hanyar jiragen-yawo lami lafiya.
Za a iya tunawa ranar sha uku ga watan nan na Disamba, NAHCON ta sanar da dakatarwa ta wani dan-lokaci don tsagaita raba kujerun tafiya Hajjin bana ga kampanonin-jigilar Maniyyata. Anyi hakan don kwatanta rabo na Allah da Annabi, biyo bayan korafe-korafe da suka bijiro daga wasu bangarori.
Sanarwar tace NAHCON na nan kan wannan tsaikon har sai ta tabbatar da gaskiyar lamari don samun Rabo na gaskiya ga dukkan kamfanonin na jigilar Alhazan.