Hajj 2024 : Hukumar Alhazai Ta Bauchi Ta Siyar Da Kujerun Haji Guda 1700- Imam Abdurrahman

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi ta sayar da kimanin guraban kujerun aikin hajji akalla *1700* daga cikin guda *3364* da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta ware wa Jihar Bauchi.

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, yace Sakataren zartarwa na hukumar jindadin alhazan ta jihar Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris,shi ne bayyana hakan yayin  zantawarsa da manema labarai kan shirye shiryen aikin hajji daga Bauchi, inda yace wayarda alumma kan sabbin tsare tsaren aikin hajjin na shekarar 2024 daya gudana a jihar Bauchi yayi tasiri kwarai da gaske.

Imam Abdurrahman ya alakanta nasarar gudanar da atisayen wayarda kan alummar ne da irin gudumawa da goyon bayan da tsarin ya samu daga sarakunan mu na jihar Bauchi da shugabannin kananan hukumomi da limamai da sauran masu ruwa da tsaki a aikin Hajji.

Ya kara da cewa sabbin tsare-tsare na Saudiyya kan ayyukan Hajji na shekarar 2024 ne suka tilastawa kasashe fara  shirye-shiryen ayyukan Hajjinsu da wuri.

 Imam Abdurrahman ya ci gaba da tunatar da cewa NAHCON ta sanya *N4.5M* a matsayin kudin ajiya na bana tare da bayar da wa'adin watan Disamba na tura kaso na farko daga dukkan Jihohin a kasa domin su kare  gurbin kujerun  aikin Hajji da aka ware musu.

A cewar sa "a baya dai mun aiyana karshen watan Disamba na 2023 a matsayin wa'adin karban kudin ajiyar aikin hajjin 2024, zamu saurari hukumar alhazai ta kasa don jin umurni na gaba"

Imam Abdurrahman ya shawarci maniyyata dasu yi anfani da wannan lokaci na musamman wajen cikita kudin ajiyarsu na N4.5M, harilayau sabbin masu biya, suma dama ce garesu dasu biya kudin ajiyar tasu.

 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki