Sojoji Sun Kutsa Ofishin EFCC Dake Kuduna Domin Kubutar Da Abokan Aikinsu

Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu jami'an sojin saman ƙasar suka kutsa ofishinta da ke Kaduna domin ƙwato 'yan uwansu da hukumar ta tare bisa zargin 'karya dokar aikin tsaro'.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun jami'ain hulɗa da jama'a na hukumar, Dele Oyewale, ta ce a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba jami'an EFCC sun kama wasu mutum biyar da hukumar ke zargi da aikata laifukan da suka shafi zambar kuɗi ta intanet a unguwar Barnawa da ke birnin Kaduna

Hukumar ta ce ta kama mutanen ne ba tare da wani tashin hankali ba, daga nan ne kuma wasu mutum shida - da suka haɗar da sojoji huɗu da ɗaliban cibiyar fasahar aikin sojin sama biyu - waɗanda ke wurin a lokaci da aka kama waɗanda ake zargin, suka yi wa ofishin EFCC da ke Kaduna ƙawanya da nufin tilasta sakin mutanen.

''Daga nan ne kuma aka kama su tare da tsare su a ofishin hukumar, bisa zargin karya dokar aiki tsaro", kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

A yayin da ake tare da mutanen hukumar EFCC ta ce ta tuntuɓi rundunar sojin sama ta ƙasa inda hukumomin biyu ke tattanawa domin warware lamarin.

Dele Oyewale ya ce a ranar Juma'a wasu jami'an sojin sama sun dirar wa ofishin EFCCn da ke Kaduna a cikin shirin faɗa, don tilasta sakin abokan aikin nasu.

"Hukumar EFCC ta yi aiki cikin nutsuwa, inda ta ci gaba da tattaunawa da jagororin rundunar sojin saman, kuma daga ƙarshe aka cimma matsayar sakin sojojin bayan an ɗauki bayansu", kamar yadda mai magana da yawun EFCCn ya bayyana.
(BBC HAUSA)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki