Hukumar Tace Finafinai Ta Rufe Sutudiyon Mawaki Ɗanzaki

Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa ita ce ta garƙame sutudiyon mawakin siyasar nan Idris Ɗanzaki tare da yin awon gaba da kayan aikinsa.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Abdullahi Lawan Sulaiman ya shaida wa ’yan jarida a Kano cewa hukumar ta ɗauki matakin ne bayan mawaƙin ya yi biris da gayyatar da ta yi mana na bayyana a ofisoshint

Ya ce tun ranar Asabar Hukumar ta nemi mawakin ya bayyana a ofisoshinta, amma har zuwa lokacin da muke kawo muku wannan labari bai amsa gayyatar ba.

“Kasancewar a yanzu zamani ya sawwake abubuwa mun yi amfani da waya inda muka kira wannan mawaki Idris Ɗanzaki inda kuma muka nemi ya zo wannan hukuma.

“Bayan sun kira ni a waya sun ce suna gayyata ta, na tura lauyana hukumar don ya wakilce ni.

“Amma me zai faru sai aka kira ni cewa wai hukumar ta rufe sutudiyona haka kuma ta kwashe wasu kayayyakin aikina.”

Abdullahi Lawan ya kara da cewa hakan ya sa Hukumar ta sa aka kulle sutudiyon tare da kwashe kayayyakin aikinsa.

Sai dai yayin da majiyarmu ta tuntubi mawaƙin ya tabbatar mata cewa hukumar ta gayyace shi amma ya tura lauyansa ya wakilce shi.

Mawakin ya yi iƙirarin cewa Hukumar ba ta sanar da shi laifin da take zargin sa da aikatawa ba.

Duk da cewa hukumar ba ta bayyana dalilin gayyatar mawakin ba, amma rahotanni sun nuna cewa ana zargin sa ne da yin munanan kalamai ga jagoran darikar Kwankwasiyya Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a cikin wata waka da ya yi a kwanan baya.
(AMINIYA)





Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki