Gwamnatin Kano Ta nemi ƙarin tallafin haɗin gwiwa daga Gwamnatin Burtaniya.

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nemi karin hadin kai da goyon baya daga gwamnatin Burtaniya.

A sanarwar da babban sakataren yada labaransa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace, Gwamnan ya yi wannan roko ne a lokacin da ya karbi bakuncin sabon babban kwamishinan Burtaniya a Najeriya, Mista Richard Montgomery a ziyarar ban girma a ofishinsa a ranar Talata.

Ya ce bangarorin irin wannan alakar hadin gwiwa da ake bukata sun hada da Ilimi, Lafiya, Noma, gyare-gyaren hukumomi, sauyin yanayi da kuma sauye-sauyen zamantakewa.
Sauran wuraren da gwamnan ya bayyana sun hada da kiwon lafiya da ilimin mata da yara da kuma masu bukata ta musamman (Nakasassu).

Gwamnan ya kuma bayyana matukar bukatar gwamnatin Birtaniya ta ci gaba da zuba jari a jihar domin Kano na bukatar karin masu zuba jari da masana'antu daga kasashen waje.

Da yake tunawa da dorewar dangantakar da ke tsakanin Kano da gwamnatin Burtaniya, Gwamna Yusuf ya yaba da irin goyon bayan da suke bayarwa a fannoni daban-daban na ayyukan dan Adam ta ofishin bunkasa arzikin kasa da kasa (FCDO) da sauran kungiyoyi masu alaka da juna.
Daga nan sai ya yi amfani da wannan hanya wajen taya sabon jakadan Birtaniya murna, da fatan dangantakarsu da Kano za ta ci gaba da yin karfi.

Tun da farko babban kwamishinan Burtaniya, Richard Montgomery ya bayyana cewa ya je gidan gwamnati ne domin ziyarar fahimtar juna tare da samun damar tattaunawa kan bangarorin hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kano.
Babban Kwamishinan ya nuna sha’awar tallafa wa jihar a fannonin Ilimi, Lafiya, Noma, Haɗin kai a Manyan Makarantu da inganta Gwamnati da dai sauransu.

Daga nan sai ya taya gwamnati Abba Kabir Yusuf murnar nasarar da ya samu a zaben da ya share masa hanyar samun rikon shugabancinsa a matsayinsa na gwamnan jihar Kano.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki