Ganduje Ya Zama Shugaban Jami'iyyar APC Na Kasa

An nada tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

An nada Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC a taron jam’iyyar na kasa karo na 12 a ranar Alhamis a Abuja.

Haka kuma Majalisar zartarwa ta jam’iyyar ya zabi tsohon kakakin majalisar dattawa, Ajibola Basiru, a matsayin sakataren kasa.

Tsohon gwamnan na Kano ya godewa shugaba Tinubu, ya kuma yi alkawarin zage damtse, inda ya kara da cewa dimokuradiyyar cikin gida za ta yi tasiri a jam’iyyar a lokacin mulkinsa.

Gwamna Ganduje ya kuma yi alkawarin tabbatar da rijistar ‘ya’yan jam’iyyar a kimiyyance tare da mai da hankali sosai kan gudanar da zabe da magance rikice-rikice.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki